Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya

Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya

  • Diyar Sanusi Lamido, sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya, ta koka da yadda jama'a ke suka da zagi a kafafen sada zumunta ta zamani
  • Shahida Sanusi mai amfani da @shayheels a Instagram ta bayyana cewa sau da yawa ta kan so yin martani amma mutuncin kanta ta ke dubawa
  • Ta sanar da cewa ana koyon abubuwa masu tarin yawa a kafafen sada zumunta kuma mutane basu da kirki ko kadan

Shahida, diyar sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijjaniyya, Sanusi Lamido Sanusi, ta koka kan yadda ake yawan zagi da caccaka a soshiyal midiya.

"Soshiyal midiya ta na koya wa mutane abubuwa masu yawa. Mutane basu da kirki. Babu dalilin za su iya zagin ka ko caccakar ka," mahaifiyar yara biyun ta wallafa a Instagram.

Kara karanta wannan

Kambin sarauniyar kyau na kai na kuma babu yadda na iya, Shatu ta caccaki masu sukarta

Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya
Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya. Hoto daga @shayheels
Asali: Instagram
"A gaskiya, kowa ya na son yin martani. Allah ya sani, a koyaushe ina son yin martani, amma mutuncin kaina ba zai bar ni in yi hakan ba. Allah ya kare mu kuma ya ba mu karfin jure wa dukkan jarabawa."
Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya
Allah ya sani, na kan so yin martani: Diyar Sanusi II ta koka kan masu zagi da caccaka a soshiyal midiya. Hoto daga @shayheels
Asali: Instagram

Shahida Sanusi – Mahaifina ba zai daina fadin gaskiya ba koda hakan na nufin rasa kujerar sa

A wani labari na daban, Shahida Sanusi, ‘yar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta ce mahaifin ta zai ci gaba da fadin gaskiya ga masu mulki koda hakan na nufin rasa kujerar sarautar sa.

A cewar jaridar Punch, ‘yar sarkin ta yi furucin ne a yayinda take bayar da jawabi a gurin taron shekara na tunawa da yan matan Chibok wanda shekaru uku da sace su.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

Legit.ng ta tattaro inda Shahida ta ce: “Mahaifina baya tsoron sadaukar da kujerar sarautar sa indai a kan turban fadin gaskiya ne. na san cewa idan har ta kai mahaifina ga zabar daya tsakanin sarautar sa da sanin yakamatan sa, zai sadaukar da kujerar sarautar cikin farin ciki."
“Ya riga da ya cim ma burin san a gadar kakanninsa kuma zancen gaskiya yana nan yadda na san sa a matsayin ma’aikacin banki kuma shugaban babban bankin kasa. A mastayin sarki, bai chanja ba sannan kuma zai ci gaba da kasancewa yadda yake koda kuma zai zamo tsohon sarki a nan gaba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng