Shahida Sanusi – Mahaifina ba zai daina fadin gaskiya ba koda hakan na nufin rasa kujerar sa
- 'Yar sarkin Kano, Shahida Sanusi ta ce mahaifinta zai ci gaba da fadin gaskiya
- Ta ce ba zai gushe ba gurin fadin gaskiya koda hakan na nufin rasa kujerar sa
Shahida Sanusi, ‘yar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta ce mahaifin ta zai ci gaba da fadin gaskiya ga masu mulki koda hakan na nufin rasa kujerar sarautar sa.
A cewar jaridar Punch, ‘yar sarkin ta yi furucin ne a yayinda take bayar da jawabi a gurin taron shekara na tunawa da yan matan Chibok wanda shekaru uku da sace su.
Legit.ng ta tattaro inda Shahida ta ce: “Mahaifina baya tsoron sadaukar da kujerar sarautar sa indai a kan turban fadin gaskiya ne. na san cewa idan har ta kai mahaifina ga zabar daya tsakanin sarautar sa da sanin yakamatan sa, zai sadaukar da kujerar sarautar cikin farin ciki.
“Ya rigada ya cim ma burin san a gadar kakanninsa kuma zancen gaskiya yana nan yadda na san sa a matsayin ma’aikacin banki kuma shugaban babban bankin kasa. A mastayin sarki, bai chanja ba sannan kuma zai ci gaba da kasancewa yadda yake koda kuma zai zamo tsohon sarki a nan gaba.
KU KARANTA KUMA: Ni kai na ba ni da lafiya ina ga Buhari-Gwamna El-Rufai
“Lokacin da Patience Jonbathan ta kiramu yan Arewa da sunan almajirai, munyi fushi, amma idan mukayi tunani, shin bamu kasance haka ba? Muna haifan yara sannan mu watsar da su. Babu makarantun talakawa. Babu asibiti don talaka.”
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani jami'in APC ya fadi dalilin da yasa jam'iyyar sa bazata kai labari a 2019 ba.
Asali: Legit.ng