Da Dumi-Dumi: An sako Uche Nwosu, sirikin tsohon gwmana Okorocha

Da Dumi-Dumi: An sako Uche Nwosu, sirikin tsohon gwmana Okorocha

  • Yan sanda sun sako sirikin tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, bayan shafe awanni a hannun su
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan Imo, Uche Nwosu, ya shiga hannun yan sanda ne yayin da yaje coci gudanar da aikin bauta
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Imo ta bayyana cewa ba ta da masaniyar cewa an sako Nwosu a halin yanzu

Imo - Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Imo karkashin jam'iyyar AA, Uche Nwosu, ya kubuta daga hannun yan sanda, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jami'an yan sanda sun yi ram da sirikin tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a cikin coci ranar Lahadi.

Kakakin Nwosu, Nwadike Chikezie, ranar Litinin yace ya yi magana da mai gidansu, kuma yana mika godiyarsa ga waɗan da suka nuna damuwa akansa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana a kan cafke sirikin tsohon gwamna a wurin Ibada

Nwosu
Da Dumi-Dumi: An sako Uche Nwosu, sirikin tsohon gwmana Okorocha Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yace:

"Na yi magana da shi, ya na mika gaisuwarsa da godiya gare mu baki ɗaya. Yayin da muke jiran karin bayani daga hukumar yan sanda, muna kira ga mutane su kwantar da hankalinsu."
"Duk wani yunkurin ɓata ɗakin Allah to dukan mu, mun san cewa taro faɗa ne da kalubalantar Allah. Sabida haka mu bar Allah mai girma ya ɗauki mataki akan lamarin."

Shin Okoracha ya samu labari?

Mai taimakawa sanata Okorocha ta bangaren labarai, Sam Onwuemeodo, ya shaida wa Premium Times cewa sirikin mai gidansa ya samu yanci.

"Eh, yan sanda sun sako shi," inji shi.

Amma kakakin rundunar yan sandan jihar Imo, Michael Abattam, yace ba shi da masaniyar sako Nwosu.

"A hukumance, hukumar yan sandan reshen jihar Imo ba ta da masaniyar cewa an sako Nwosu."

Kara karanta wannan

'Karin bayani: 'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

Kakakin yan sandan yace hukumarsu ba zata yi wata-wata ba wajen fitar da sanarwa da zaran an sako Nwosu.

A wani labarin na daban kuma Malami ya faɗi Yadda shugaba Buhari ya ceci Najeriya daga kifewa a bayan zabe a 2015

Malami yace shugaba Buhari ya yi abin da ba kasafai shugabanni ke iya yi ba cikin shekara ɗaya da hawansa karagar mulki.

Ministan yace Buhari ya samu ƙasar nan tana tangal-tangal, kuma ya ceto ta daga kifewar tattalin arziki, wanda ka iya watsa kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262