Yan Bijilanti sun yi musayar wuta da yan binidga, sun ceto mutum 2 a jihar Kogi

Yan Bijilanti sun yi musayar wuta da yan binidga, sun ceto mutum 2 a jihar Kogi

  • Wasu yan bijilanti sun bi bayan yan bindiga bayan sun yi awon gaba da mutum biyu a gonarsu a jihar Kogi
  • Wani mazaunin yankin yace wani makocin mutanen da ya ga abin da ya faru, ya garzaya ya sanar da yan bijilanti
  • Har yanzu hukumar yan sanda ba ta ce komai game da lamarin ba, amma wani ɗan bijinti ya tabbatar

Kogi - Wata tawagar yan Bijilanti sun bi yan bindiga har cikin jeji, sun kubutar da mutum biyu, Saidu Aliyu da Usman Ibrahim a jihar Kogi.

Daily trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace mutanen ne a ƙauyen Akyara dake karamar hukumar Kogi, jihar Kogi.

Wani mazaunin ƙauyen yace lamarin ya faru ne ranar Jumu'a da misalin karfe 9:34 na safe, lokacin da mutanen suka je gona ɗebo gawayi a kan keke.

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya

Yan bindiga
Yan Bijilanti sun yi musayar wuta da yan binidga, sun ceto mutum 2 a jihar Kogi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace yayin da mutanen ke cikin ɗibar gawayin, ba zato va tsammani sai yan bindigan suka farmake su ɗauke da makamai, suka yi awon gaba da su.

Ya ƙara da cewa wani manomi da abun ya faru a idonsa, ya yi gaggawar dawo wa ciki gari ya sanar da yan Bijilanti abin da ya faru, nan take suka bi bayan maharan.

Yan Bijilanti sun gwabza da maharan

A cewar mutumin, yayin da yan bindigan suka ga yan Bijilanti sun nufo su, sai suka bude musu wuta, su ma suka maida martani.

Ƴace:

"An yi musayar wuta tsakanin yan Bijilanti da yan bindigan, inda daga ƙarshen yan bindigan suka tsere suka bar mutanen da suka sace."

Shin yan sanda sun samu rahoto?

Har yanzun kakakin yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Ovye Aya, bai ɗaga kiran waya ba kuma be turo amsar sakonnin da aka tura masa ba kan lamarin.

Kara karanta wannan

Mu'ujizar Allah ce da kubutar da ni daga hannun yan bindiga, kwamishina ya magantu

Sai dai wani jami'in Bijilanti, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace yan bindigan sun bar mutanen da suka sace lokacin da jami'ai suka ci karfin su.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Masari ya maida zazzafan Martani ga kasurgumin dan bindiga, Bello Turji

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bayyana cewa babu maganar tsagaita wuta ko sulhu tsakanin gwamnati da yan bindiga

A martanin da ya yi wa wasikar Bello Turji, kasurgumin ɗan bindigan da ya addabi arewa , gwamnan yace baki ɗaya yan bindiga maƙaryata ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: