Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya

Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya

  • Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun sake kai sabon hari gida-gida a birnin Zariya, jihar Kaduna
  • Rahoto ya bayyana cewa maharan sun shiga gidajen waɗan da suka sace da tsakar dare suna cikin bacci, suka yi awon gaba da su
  • Shugaban yankin Wusasa, Isyaku Yusufu, yace maharan sun farmaki yankin mintuna kaɗan bayan rabawar dare, suka sace mutum 8 da farko

Kaduna - Wasu miyagun yan bindiga sun fasa gida-gida a yankun Wusasa dake birnin Zariya, jihar Kaduna, inda suka sace mutum 5.

Vanguard ta rahoto cewa maharan sun farmakin yankin ne mintuna kaɗan bayan dare ya raba, inda da farko sun yi awon gaba da mutum 8.

Yan bindiga
Sabon Hari: Yan bindiga sun shiga gida-gida, sun yi awon gaba da jama'a a Zariya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban yankin Wusasa, Isyaku Yusufu, yace maharan sun shiga gida-gidan waɗan da suka sace yayin da suke bacci.

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

Malam Yusufu yace:

"Mintuna 10 bayan dare ya raba yan bindigan suka fara aikata mummunan nufin su, da farko sun tafi da mutum 8, amma yan mintuna kaɗan suka umarci yaro ɗan shekara 15, ya ɗakko yarinya yar shekara 4 su dawo gida."

Shin yan sanda sun san da lamarin?

Kakakin rundunar yan sandan Kaduna, ASP Muhammed Jalige, bai daga kiran wayar salula da wakilin Daily Nigerian ya masa ba domin jin halin da ake ciki.

A yan makonnin nan, mazauna Zariya na fama da hare-haren yan bindiga, inda wani lokacin suke tattara matafiya su yi awon gaba da su, ko su shiga gida-gida.

A ranar 8 ga watan Nuwamba, 2021, yan bindiga suka sace ma'aikatan ƙaramar hukumar Zariya 13 yayin da suke kan hanya a cikin motar Bas zuwa Giwa.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi ta kansu yayin da Yan bindiga suka bindige Basarake har lahira a Kaduna

A wani labarin na daban kuma Mafarauta sun yi wa yan bindiga kwantan bauna jihar Kaduna, sun kubutar da mutane da dama

Mafarauta a ƙauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna sun samu nasarar kama ɗan bindiga a dajin dake hanyar Birnin Gwari.

Wani mazaunin kauyen Udawa, yace Mafarautan sun samu nasarar kubutar da mutum 9 daga hannun yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262