Kaduna: Hotunan Musulmai da suka halarci coci domin taya Kiristoci murnar Kirsimeti
- Musulmai masu tarin yawa sun garzaya coci a cikin garin Kaduna domin taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti
- Fitaccen fasto, Yohanna Buru, ya nuna jin dadinsa da godiya inda ya karba Musluman hannu bibbiyu yayin da suka kai ziyarar
- A cewar Buru, wannan al'amarin zai tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da hakurin addini a fadin jihar Kaduna
- Alhaji Rabo Abdullahi, hakimin Kurmin Mashi da ke Kaduna, ya nuna jin dadinsa kan yadda ya ga matasa da malamai sun halarci cocin
Kaduna - Daruruwan Musulmai sun taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti yayin da suka halarci bikin a coci domin habaka hadin kai, zaman lafiya da kuma hakuri a jihar Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban babbar cocin Christ Evangelical and Life Intervention da ke Kaduna, Fasto Yohanna Buru, wanda ya karbe su ya bayyana murnarsa kan yadda suka halarci cocin.
Ya ce, duk da kalubalen tsaro, cutar korona da kuma yawan kudin mota, Musulmai da suka hada da mata sun samu lokacin halartar cocin da niyyar inganta alaka mai kyau, fahimtar juna da kuma soyayya.
Kamar yadda yace, wannan ne karo na goma da suka karba bakuncin Musulmai daga jihohi daban-daban a ranar Kirsimeti.
Fitaccen faston ya ce, dukkan Musulmai da suka halarci wurin bautar sun hada da Musulmai masu akidun Tijjaniya, Shi'a, Kadriyya da Sunni.
Hakimin Kurmin Mashi, Alhaji Rabo Abdullahi, ya ce ya yi matukar murna ganin yawan matasa Musulmi da limamai da suka halarci cocin, Daily Trust ta ruwaito.
Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023
A wani labari na daban, a jiya Juma'a, hafsoshin tsaro sun samu sabon umarni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa su mitsike 'yan ta'addan ISWAP, wadanda suka maye gurbin Boko Haram a ta'addancin arewa maso gabas, kafin shekarar da wa'adin mulkinsa zai cika.
The Nation ta ruwaito cewa, Buhari ya bayar da wannan umarnin a taron majalisar tsaro da suka yi a Abuja, sa'a ashirin da hudu bayan da 'yan ta'addan suka yi ruwan makamai masu linzami a filin jirgin sama na Maiduguri kafin isar shugaban kasa garin.
Mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu sakamakon harba makaman masu linzami.
Asali: Legit.ng