An kori ma'aikatan gwamnatin Kano 4 daga aiki saboda takardun bogi
- Hukumar Kula da Ma'aikata ta Jihar Kano ta sallami wasu ma'aikata hudu daga bakin aiki bayan samun su da laifin bada bayanan karya da amfani da takardun bogi
- Injiiya Bello Mohammad, shugaban hukumar kula da ma'aikatan ne ya bayyana hakan ta bakin kakakin hukumar, Ismail Gwammaja
- Har wa yau, hukumar ta kuma yi wa wasu ma'aikata kimanin 126 karin girma da mataki cikinsu da direktoci, mataimakan direktoci da manya da matsakaitan ma'aikata
Jihar Kano - Hukumar kula da ma'aikata na Jihar Kano ta sallami a kalla mutane hudu daga aiki saboda samunsu da gabatar da takardun bogi da yin karya a wasu bayanansu, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban hukumar, Injiiya Bello Mohammad ne ya bayyana hakan cikin wata takarda da kakakin hukumar, Ismail Gwammaja ya raba wa manema labarai bayan taron yi wa manyan ma'aikata karin girma da aka yi a dakin taron hukumar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An yi wa ma'aikata 126 karin girma, Mohammed
Hakazalika, Mohammed ya kuma ce kimanin ma'aikata guda 126 ne aka yi wa karin girma a hukumomi daban-daban a jihar Kano kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya bada karin bayani kamar haka:
"Mutum biyar masu mukamin mataimakin direkta a mataki na 15 an musu karin girma zuwa direktoci a mataki na 16, yayin da mutum 36 da ke mataki na 14 an musu karin girma zuwa mataimakan direkta a mataki na 15 sai wasu kuma manya da matsakaitan jami'ai da ake yi wa karin a karshen watan Disamban 2021.
"Hukumar ta kuma duba batun ladabtar da wasu mutane hudu da aka samu da laifin gabatar da takardun bogi da yin karya a wasu takardunsu.
"Muna kira ga dukkan ma'aikata a jiharmu su zage damtse su kuma zama masu gaskiya yayin gudanar da ayyukansu."
Tunda farko, Sakataren dindindin na hukumar, Alh Sani Abdullahi Kofar Mata ya jadada bukatar da ake akwai na ma'aikata su zama masu basira su kuma bawa aikinsu muhimmanci tare da tsoron Allah.
Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa
A wani labarin, gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.
A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'
Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.
Asali: Legit.ng