Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

  • Wani takarda daga Hukumar Shige da Fice na kasa, NIS, da ya fito ya nuna cewa 'yan ta'adda daga kasashen suna shirin kawo hari a birnin tarayya Abuja a lokacin hutun Kirsimeti
  • Takardan mai dauke da sa hannun kwantrolla na Immigration, Edrin Okoto, a madadin Kwantrola Janar na kasa, Idris Jere, an turo ta ne ga kwantrololi masu kula da iyakokin Najeriya na ruwa, sama da kasa
  • Mai magana da yawun hukumar, NIS, Amos Okpu, ta tabbatar da sahihancin takardar amma ya nuna rashin jin dadinsa kan fitar da takardar ta sirri

Hukumar Kula da Shige da Fice na kasa, NIS, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar 'yan ta'adda na kasashen waje su kawo hari a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

Kamar yadda ya ke cikin takardan bayannan gwamnati da aka gano a ranar Alhamis, ana shirin kai harin ne tsakanin ranar 17 ga watan Disamba zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Takardan mai kwanan wata ta ranar 23 ga watan Disamban 2021 na dauke da sa hannun Kwantrola na Immigration, Edrin Okoto.

Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja
'Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari a Abuja. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An fitar da takardar ne a madadin Kwantrola Janar na Immigration, Idris Jere, don aika wa sauran kwantrololi da ke iyakokin kasa, sama da ruwa a sassan kasar da kuma kwamandoji masu sintiri a iyakokin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashi na takardar ya ce:

"Ofishin mukadashin Kwantrolla Janar na Kasa, CGI, ta samu wani rahoton tsaro daga fadar shugaban kasa, OSGF.
"Rahoton ya shafi barazanar kawo hari ne a babban birnin Najeriya, Abuja daga ranar 17 zuwa 31 ga watan Disamban 2021.
"Wani dan kasar Algeria DRAHMANE, OULD ALI, da aka fi sani da Mohammed Ould Sidat zai jagori harin tare da taimakon wani Zahid Aminon, dan kasar Nijar."

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

A cewar takardar, yan kasar wajen suna shirin shigowa Najeriya ne daga Mali ta Nijar, kuma suna da wasu masu taimaka musu wanda a yanzu suna Najeriya.

Takardar ta umurci jami'ai da ke iyakokin Najeriya su tsananta bincike a dukkan iyakoki na kasa, sama, ruwa da sa ido kan mutane da ababen hawa don kama yan ta'addan da ke shirin kawo hari Abuja.

Kakakin Hukumar NIS, Amos Okpu, ta tabbatar da sahihancin takardar amma ya nuna rashin jin dadinsa kan wani/wata ya fitar da takardar ta sirri.

Ya bada tabbacin cewa jami'ansu da ke iyakoki za su iya yin aikinsu yadda ya dace yana mai kira ga mutanen Abuja su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Ya ce:

"Babu bukatar mutane su tada hankulansu. Ina tabbatar muku jami'an mu da ke iyakoki za su tabbatar sun kama yan ta'addan idan suka yi yunkurin shigowa kasar.
"Tuni mun fara aiki tare da sauran hukumomin tsaro a kan batun."

Kara karanta wannan

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

Ku saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164