Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba

Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki wani masallaci da ke garin Tella na karamar hukumar Gassol a jihar Taraba
  • Masallatan suna tsaka da sallar Isha'i 'yan bindigan suka zagaye su tare da tasa keyar hudu daga cikinsu
  • Wani mazaunin yankin, Suleiman Rabiu, ya sanar da cewa wurin karfe 7:12 na dare miyagun suka zagaye masallacin

Gassol, Taraba - 'Yan bindiga sun kai farmaki har cikin masallaci da ke garin Tella a karamar hukumar Gassol ta jihar taraba inda suka yi garkuwa da masallata hudu.

Wani mazaunin Tella, Suleiman Rabiu, ya sanar da Daily Trust cewa 'yan bindigan sun kai su 12 da suka zagaye masallacin wurin karfe 7 da minti 12 kuma sun sace masallatan yayin da suke tsaka da sallar Isha'i.

Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba
Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: Original

Majiyar ta ce 'yan bindiga sun katse wa jama'a sallar inda suka tasa keyar masallatan da bindiga a kansu.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a maboyarsu, sun samo shanu da miyagun makamai

Daily Trust ta ruwaito cewa , 'yan bindigan daga baya sun saki mutum daya tare da yin awon gaba da sauran zuwa inda babu wanda ya sani.

Daga cikin wadanda aka sace akwai Alhaji Yahaya, Aminu Dali da Alhaji Hussaini, wanda shi ne shugaban masu kasuwanci hatsi na yankin.

Mazaunan yankin Gassol suna fuskantar farmakin 'yan bindiga wadanda ake zargin suna komawa yankin daga jihar Zamfara sakamakon matsanta musu da sojoji suka yi.

A cikin makonni uku da suka gabata, sama da mutane 25 da suka hada da 'yan kasuwa da manoma ne aka dinga sacewa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da farmakin masallacin amma bai sanar da dalla-dallan yadda lamarin ya faru ba.

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

A wani labari na daban, fusatattun jama'ar jihar Katsina sun mamaye babban titin Funtua zuwa Sheme na jihar Katsina tare da hana ababen hawa wucewa a titin Funtua zuwa Gusau kan farmakin da 'yan bindiga ke kai musu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wani matafiyi mai suna Imam Abubakar, ya sanar da cewa matafiya suna nan dankare a wurin sun kasa yin gaba ko baya.

"Ga mu nan a wurin, ba zan iya fadin yawan ababen hawa da ke titin nan ba da masu zanga-zanga suka tare. A yanzu da muke magana, muna jin harbin bindigar 'yan sanda dasojoji wadanda aka turo yankin, amma masu zanga-zangar sun rufe titin suna kona tayoyi," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng