Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta maye gurbin lambobin NIN da wani abun daban
- Ana bukatar 'yan Najeriya da su maye gurbin lambar shaidar zama dan kasa ta NIN da ake amfani dashi yanzu da wasu sabbin lambobin zamani na digitoken
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana hakan ne a cikin wani dan littafi da Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) ta fitar.
- Hukumar ta kuma ce tabbatar da lambar NIN daga kowane kamfani ko hukuma zai zama wani laifi ne abin hukuntawa
Abuja - A ranar Laraba, 22 ga watan Disamba ne gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na bullo da wata lambar alama da za ta maye gurbin lambobi 11 da ake da su a halin yanzu na NIN.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnati ta ce daga watan Janairun 2022, sabuwar lambar alamar za ta zama madadi ga NIN ga duk 'yan Najeriya a fadin kasar.
A cikin wani dan littafi da Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) ta fitar, gwamnatin Najeriya ta ce zai zama doka idan aka gano wani kamfani ko hukuma na tabbatar da NIN a ayyukansu.
A cewar gwamnatin Najeriya, tabbatar da NIN a kowace hukuma ko kamfani zai zama wani laifi da zai zama abin hukuntawa.
Yaya wannan sabuwar lambar alama da FG za ta gabatar take?
Har ila yau, jaridar Vanguard ta ba da rahoton cewa sabuwar lambar alamar za ta kunshi haruffa 16 hade da lambobi.
Ba a tura vNIN kuma wa'adinsa na karewa bayan awanni 72
Hakanan an ce kamfanoni kawai za a ba su izinin adanawa da tabbatar da vNIN ne wanda aka kebe ga mai rike da shaidar tare da NIN.
Dan littafin ya bayyana a wani sashin:
"Mai rike da ID wanda ya shigar da shaidar NIMC dinsa ta manhajar MobileID ta wayar hannu ko kuma aka samar ta hanyar danna lambobin USSD ne ke bayar da NIN na yau da kullun."
Hakazalika, sabuwar lambar alamar za a yi iya tabbatar da ita ne ta bin wasu kebabbun hanyoyin da hukumar ta NIMC ta amince dasu.
Littafin ya kuma yi karin haske cewa iyaye za su iya amfani da bayanan su don samar da NIN na yau da kullum ga ’ya’yansu kanana kan waccan manhajar ta NIMC.
FG ta fitar da muhimmin bayani akan rajistar NIN
Gwamnatin tarayya ta samu ci gaba abin a yaba a kokarinta na samar da rumbun adana bayanan 'yan Najeriya.
Akalla kimanin 'yan kasa miliyan 51 ne aka yi musu rajistar NIN tun daga shekarar 2020.
Hakazalika, gwamnati ta bayyana cewa an yi rajistar layukan waya sama miliyan 189 zuwa yanzu.
A baya, hukumar NIMC, ranar Alhamis, ta sanar da cewa yan Najeriya sama da miliyan 60m sun yi rijistar lambar NIN, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Punch ta ruwaito cewa ya zuwa yanzun NIMC na da bayanan wannan adadin na yan Najeriya a kunshin ajiye bayananta (NIDB).
Hukumar ta kara da cewa an samu wannan nasarar ne da hadin kan masu ruwa da tsaki a bangaren, wanda ya hada da gaba daya yan Najeriya.
Asali: Legit.ng