Da duminsa: Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

Da duminsa: Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami filin jirgin sama da ke Ngomari a babban birnin jihar Borno
  • Wannan lamarin ya faru ne yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kan hanyarsa ta zuwa jihar domin kaddamar da wasu ayyuka
  • Daya daga cikin makaman masu linzami ya tsallaka har zuwa yankin Ajilari, kusa da sansanin sojojin Najeriya da ke Maiduguri

Maiduguri, Borno - 'Yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Kara karanta wannan

Da duminsa: NCAA ta garkame babban ofishin Glo na Abuja kan bashin N4.5bn

Da duminsa: Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri
Da duminsa: Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari.

Alamu suna nuna cewa, maharan sun daidaita tare da saitar filin saukar jiragen saman ne saboda makaman sun sauka 10:45 na safe, mintoci kadan kafin isar Buhari birnin.

Wasu mazauna yankin sun sanar da Daily Trust cewa, maharan sun auna musu makamai masu linzamin inda suka kashe mutanen da ba a san yawansu ba tare da tarwatsa kadarorin jama'a.

Wani mazaunin yankin ya ce daya daga cikin makaman ya fada wani ofishi na kusa yayin da biyu suka fada yankin ngomari Ayashe inda suka halaka yara hudu.

"Zan iya tabbatar muku da cewa Walida mai shekaru goma sha shida ta riga mu gidan gaskiya sakamakon harin. A take ta rasu, ta na girki ne daidai lokacin da makamin ya tarwatsa kan ta," yace.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

A kalla mutane 25 ne suka samu miyagun raunika a farmakin, har a halin yanzu hukumomi ba su yi tsokaci a kan lamarin ba.

Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis zai ziyarci babban birnin jihar Borno, Maiduguri, cewar Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Zulum wanda ya sanar da hakan yayin da ya je duba aikin gadar sama ta Maiduguri, ya yi kira ga mazauna jihar da su fito kwansu da kwarkwata wurin karbar Shugaban kasa Buhari hannu bibbiyu.

Ya ce shugaban kasan zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka hada da gadar sama da kuma tituna. Zai kaddamar da CDL na jami'ar Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng