Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya bar Aso Villa, Ya kama hanyar zuwa Maiduguri
- A yau Alhamis, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewacin Najeriya
- Yayin wannan ziyara ana sa ran shugaban ƙasan zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Zulum ya fara kuma ya kammala
- Rahoto daga fadar shugaban ƙasa, ya bayyana cewa Buhari ya nufi filin jirgin Nnamdi Azikwe, inda zai kama hanyar Borno
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito daga fadarsa Aso Villa, zuwa filin jirgin Nnamdi Azikwe, inda zai kama hanyar zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
A cewar wakilin jaridar Punch, shugaba Buhari ya bar harabar fadar shugaban ƙasa ne da misalin ƙarfe 10:04 na safiyar Alhamis.
Shugaban ƙasa zai kai ziyarsa jihar Borno ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya fara kuma ya kammala.
Abubuwan da Buhari ya yi a Borno
A ranar Talata, gwamna Zulum na jihar Borno yace shugaba Buhari ya tallafa wa al'ummar jihar kuma ya sadaukar da kansa wajen ganin mutane sun rayu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ƙara da cewa Buhari ya kashe kuɗaɗe dala miliyan $50m domin tabbatar da al'ummar Borno sun samu hasken wutar lantarki.
Bayan haka, Zulum ya yi kira ga mutanen jihar Borno su fito kwansu da kwarkwata su tarbi shugaba Buhari hannu biyu kasancewarsa uban ƙasa, kamar yadda dailytrust ta rahoto.
Osinbajo zai jagoranci FEC
Yayin da Buhari ya kama hanyar zuwa jihar Borno, mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, na can yanzu haka yana jagorantar taron majalisar zartarwa (FEC).
Duk da gudanar da taron jiya Laraba kamar yadda aka saba, a yau Alhamis ana cigaba da taron FEC na musamman domin duba wasu batutuwa da suka shafi gwamnatin tarayya.
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shirin gwamna Ganduje na ficewa daga jam'iyyar APC
Bayan hukuncin kotu har sau biyu kan rikicin APC a Kano, an fara jita-jitar cewa gwamna Ganduje zai fice daga APC.
Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa wannan labarin ƙanzon kurege ne.
Asali: Legit.ng