Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shirin gwamna Ganduje na ficewa daga jam'iyyar APC

Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shirin gwamna Ganduje na ficewa daga jam'iyyar APC

  • Bayan hukuncin kotu har sau biyu kan rikicin APC a Kano, an fara jita-jitar cewa gwamna Ganduje zai fice daga APC
  • Kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa wannan labarin ƙanzon kurege ne
  • Yace har yanzun Ganduje shine jagoran APC a jihar Kano, kuma tsaginsa bai hakura ba, zai ɗaukaka ƙara zuwa gaba

Ƙano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba zai fice daga jam'iyyar APC ba biyo bayan rushe shugabannin APC na tsaginsa.

Premium Times tace jita-jita ta watsu sosai cewa Ganduje ya fara tattaunawa da magoya bayansa, neman shawara yayin da yake shirye-shiryen fita daga APC.

Rahoto ya bayyana cewa gwamnan na shirin barin APC ne saboda hedkwatar jam'iyya ta ƙasa ta ƙi goyon bayansa a rikicin APC reshen Kano.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Wani babban jigon jam'iyyar APC ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Gwamna Ganduje
Gwamnatin Kano ta yi bayani kan shirin gwamna Ganduje na ficewa daga jam'iyyar APC Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Gwamnatin Kano ta musanta

Sai dai kwamishinan birane da raya karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya musanta rahoton sauya shekar Ganduje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso ya shaida wa BBC Hausa cewa jita-jitar ƙarya ce tsagwaronta kuma har yanzun gwamnan shine jagoran APC a jihar Kano.

Kwamishinan yace:

"Waɗan da ke yaɗa wannan jita-jitar ne ke shirin sauya sheka daga APC ga dukkan alamu. Ta ya gwamna mai ci zai fice daga jam'iyyarsa yayin da tsohon gwamna, wanda ya shigo APC, ya zama jagora na jiha?"
"Ta ya gwamnan da ya jima a cikin jam'iyya zai fice ya koma wata jam'iyya saboda rikicin cikin gida?"
"Jam'iyyar APC ta mu ce, kuma har wa yau zamu cigaba da jawo sauran mambobi a jiki domin zaman lafiya, kuma zamu sasanta mu magance rikicin nan."

Wane mataki Ganduje zai ɗauka?

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Game da hukuncin kotu, Mista Kwankwaso, wanda ya yi kaurin suna wajen sukar tsagin Shekarau a kafafen watsa labarai, yace Ganduje zai ɗaukaka ƙara.

A baya mun kawo rahoton yadda jam'iyyar APC ta gudanar da zaben shugabannin ta guda biyu a reshen jihar Kano a watan Oktoba.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Masari ya sha alwashin kawo karshen ta'addancin yan bindiga a arewa kafin dauka mulki a 2023

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace zasu haɗa karfi su murkushe yan bindiga a jihohin arewa da abun ya shafa kafin wa'adin mulkinsu ya ƙare a 2023.

Gwamnan, wanda ya faɗi haka yayin rattaba hannu kan kasafin kudin 2022 ranar Laraba a Katsina, yace ba gudu ba ja da baya a yaƙi da ayyukan yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel