Ba gudu ba ja da baya sai mun kawo karshen yan bindiga a Arewa, Gwamna
- Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 da ya kai biliyan N323.3bn
- Masari ya sha alwashin kawo ƙarshen ta'addancin yan bindiga a jihohin arewa da abun ya shafa kafin wa'adin 2023 ya cika
- Yace wajibi kowa ya shirya kalubalantar waɗan nan sheɗanun mutanen, ya nuna musu a shirye yake ya kare yankinsa
Katsina - Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace zasu haɗa karfi su murkushe yan bindiga a jihohin arewa da abun ya shafa kafin wa'adin mulkinsu ya ƙare a 2023.
Gwamnan, wanda ya faɗi haka yayin rattaba hannu kan kasafin kudin 2022 ranar Laraba a Katsina, yace ba gudu ba ja da baya a yaƙi da ayyukan yan bindiga.
Dailytrust tace kasafin biliyan N323.3bn da ya sa wa hannu ya zama doka, ya yi ƙasa da asalin biliyan N341bn da gwamnan ya miƙa wa majalisar dokoki.
Gwamna Masari yace:
"Ya zama wajibi kowa ya shirya maida martani na yaƙar yan bindiga saboda su shaiɗanu ne dake wakiltar sheɗan. Bai kamata mu nuna gajiyawa ba a wannan yaƙin."
"Mun karbi mulki a dai-dai lokacin da ake fuskantar babbar barazanar tsaro a 2015, kuma da izinin Allah ba zamu mika mulki ga shugabannin gaba a halin nan ba, wajibi mu dawo da zaman lafiya."
"Babbar hanyar da zamu kalubalanci waɗan nan mutanen shi ne mu nuna musu mun shirya, zamu kare yankin mu, rayukan mu da dukiyoyin mu."
Yadda majalisa ta rage kasafin 2022 a Katsina
Tun da farko kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Alhaji Tasi’u Maigari, ya bayyana irin matakan da suka bi kafin amincewa da kasafin kudi na 2022.
Yace sai da majalisa ta tuntubi kungiyoyi masu zaman kansu, mazabun su, da kuma al'ummar jihar kafin amincewa da kasafin.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Kogi ya sha alwashin babu dan ta'addan da zai shigo jiharsa ya fita a raye
Gwamna Yahaya Bello ya yi alƙawarin cewa duk wani ɗan ta'adda da ya shiga jihar Kogi ba zai fita da rayuwarsa ba.
Yace gwamnatinsa a shirye take ta ɗauki tsattsauran mataki kan bara gurbin dake shigowa jihar domin tada zaune tsaye.
Asali: Legit.ng