Addu'a da yawaita Azumi ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Sheikh Kabara

Addu'a da yawaita Azumi ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Sheikh Kabara

  • Sheikh Qariballah Nasiru Kabara ya bayyana cewa mutane du dage da addu'a da kuma.yawan azumi kan matsalar tsaro
  • Malamin yace matukar mutane suka rungumi yin haka a kowane lokaci, to Allah zai kawo karshen duk wasu matsaloli
  • Shehin yace kowa ya koma ya duba tsakaninsa da Allah, ya tuba ya daina duk wasu ayyuka mara kyau

Kano - Malamin addinin musulunci kuma jagora a ɗariƙar Qaɗiriyya, Shiekh Qariballah Nasir Kabara, ya kira yi yan Najeriya su dage da addu'o'i da Azumi da kuma neman yafiyar Allah.

Malamin yace haka ne kaɗai zai sa Allah mai girma da ɗaukaka ya kawo ƙarshen matsalar tsaron da mutane ke fama da shi, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A cewar shehin malamin halin rashin tsaro da Najeriya ke fama da shi da sauran wasu ƙasashen duniya babban abin damuwa ne.

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Sheikh Kabara
Addu'a da yawaita Azumi ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Sheikh Kabara Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Yace ko dan haka ya kamata mutane su gyraa tsakaninsu da Allah kuma su nemi yafiyarsa ko hakan zai kawo karshen duk ayyukan ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin ya yi wannan furuci ne yayin gudanar da addu'o'in neman zaman lafiya a ƙasa, wanda ya gudana a Darul Qadiriyya Kano.

Yace:

"Ya kamata mu koma mu gyara tsakanin mu da Allah da ya halicce mu, mu tuba mu watsar da muggan laifukan da muke masa. Mu taimaki mabuƙata kuma mu kara girmama iyaye."
"Zurfin tunani kan abin da muke aikata wa tsakanin mu da Allah da kuma mu'amalar mu da mutane da niyyar gyara zai taimaka wajen samun sakamako mai kyau."

Addu'a ce kaɗai maganin kunci

Sheikh Kabara ya shawarci mutane su rungumi addu'a a kowace rana kuma su gina kyakkyawan alaƙa tsakanin su da mahalincinsu.

Daga nan kuma sai ya bukaci baki ɗaya al'ummar musulmi na faɗin Najeriya da duniya baki ɗaya su dage da addu'a domin samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

A wani labarin na daban kuma Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.

A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262