'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba

'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba

  • Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce bai yarda da shirin gwamnati na sauya wa yan ta'adda halaye ba tare da mayar da su cikin mutane
  • Gwamnan ya ce babu wani tubabben dan ta'adda sai dai wanda ya mutu don haka ya ce shi abin da ya ke so shine a rika kashe yan ta'addan kawai
  • El-Rufai ya bayyan hakan ne yayin zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a Abuja yayin da ya ziyarci Shuagba Buhari don masa bayani kan harin da yan ta'adda suka kai Kaduna

FCT, Abuja - Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya ce, bai yarda da tsarin sauya wa 'yan ta'adda hali ba, ya kara da cewa hanyar da ta fi dace wa a bi da su kawai shine su 'tafi su gamu da Allah'.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabon Ministan da Buhari ya tura mata

Gwamnan ya bayyana matsayarsa kan batun ne a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawa da Shugaba Muhamamdu Buhari, The Cable ta ruwaito.

'Mu aika su lahira su hadu da Allah' - El-Rufai ya ce bai san wani zancen tubabbun 'yan ta'adda ba
El-Rufai ya ce tubabben dan ta'adda shine kawai wanda ya mutu. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya kai ziyara gidan gwamnatin ne domin yi wa Shugaba Buhari bayani kan harin baya-bayan da yan ta'adda suka kai inda suka kashe mutum 40 a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya yi wa gwamna El-Rufai rakiya zuwa gainin Buhari.

Ya ce:

"Babu wani abu mai suna tubabbun yan ta'adda. Dan ta'addan da ya tuba kawai shine wanda ya mutu. Niyyar mu shine mu kashe su (yan ta'addan), su tafi su ga Allah."

El-Rufai ya ce an sun san inda yan ta'addan suke boye wa amma sojoji suna duba fararen hula da ka iya mutuwa ne idan an ce za a far musu a inda suke.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Akwai 'yan ta'adda iri uku a Najeriya, El-Rufai

Gwamnan ya ce akwai yan ta'adda iri uku: Yan Boko Haram, Yan Bindiga da Yan Kungiyar IPOB kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda da aka yi a baya bayan nan ya bawa sojoji daman ragargazarsu da yakarsu.

El-Rufai ya bakuci shugaban kasa ya sake tura jami'an tsaro uwa Kaduna domin samun daman magance matsalar.

Ya yi kira ga jami'an tsaro su kara zage damtse wurin ragargazan 'yan ta'addan.

Bayan Shan Luguden Wuta, ’Yan ISWAP Sun Birne Mayakansu 77 a Marte

A wani labarin, kun ji cewa bayan shan luguden wuta da ragargaza, mayakan ISWAP sun birne ‘yan uwansu guda 77 a wuraren yankin Marte, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda rahotanni daga PRNigeria su ka nuna, an halaka mayakan ne sakamakon farmaki da sojojin saman Najeriya su ka kai sansanayen ‘yan ta’addan guda uku da ke wuraren tafkin Chadi.

An samu bayanai akan yadda sojojin su ka lalata musu bindigogin yaki da babura da dama yayin farmakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164