Da Dumi-Dumi: Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri kan sabon kundin zaben 2021
- Majalisar dattawa ta shiga taron sirri a Abuja biyo bayan kin amincewar Shugaba Buhari da sabon kundin dokokin zaɓe 2021
- A jiya ne shugaba Buhari ya aike wa majalisar da sakon kin amincewarsa da kundin, saboda wasu dalilai
- Har yanzun dai babbar majalisar ƙasa ba ta kammala aiki kan kasafin kudin shekarar 2022 ba
Abuja - Majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta shiga ganawa biyo bayan samun sako daga fadar shugaban kasa kan kudirin gyara kundin zaɓe 2021.
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike wa da majalisar wasika kan kudirin da suka kai gabansa, inda yaƙi amincewa da garambawul din.
Leadership ta rahoto cewa gyaran da akai wa kundin zaben 2021, ya kunshi wajabta wa jam'iyyun siyasa gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye (yar tiƙe).
Kwanaki 30 da doka ta baiwa shugaba Buhari ya rattaɓa hannu ko ya ƙi amincewa da shi sun ƙare ranar Lahadi 19 ga watan Disamba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahotanni sun bayyana cewa Sanatocin sun shiga taron ne da misalin karfe 10:44 na safiyar ranar Talata 21 ga watan Disamba.
Wannan taron na su dai ba zai rasa alaƙa da sabon kundin zaben 2021, kasafin kudin 2022 da kuma tantance sabon minista daga jihar Taraba.
Abinda ya jawo tsaiku a kasafin 2022
A jadawalin da majalisar ta tsara, tun a makon da ya gabata ya kamata ta kammala aiki kan kasafin kudi 2022 amma ta ɗage zuwa wannan makon.
Sai dai sanatocin sun bayyana cewa hakan ta faru ne saboda rashin saka kasafin hukumar zaɓe INEC na zaɓen 2023 da kuma kudin kidayar da ake shirin gudanar wa a 2022.
Wata majiya ta bayyana cewa an samu tsaikon ne daga rashin ɗaukar mataki kan garambawul din dokokin zabe da fadar shugaban ƙasa ta yi kuma shi ne ya tilasta wa yan majalisun ɗage wa zuwa wannan makon.
A wani labarin kuma Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023
Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC , Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargaɗin cewa matukar ba'a shawo kan matsalar tsaro ba, babban zaben 2023 ba zai yuwu ba.
Jega yace wajibi a tunkari tsaron kasar nan dagaske, idan kuma ba haka ba babu jam'iyyar da zata amince da zaɓen 2023 da zaa gudanar.
Asali: Legit.ng