'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu

'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da ceto wasu mutum 2 daga hannun masu garkuwa da mutane tare da kwato wasu shanun sata
  • Kamar yadda kakakin rundunar ya sanar da manema labarai, 'yan daba ne ke tare mutane a kan babban titin Ajaokuta zuwa Itobe a jihar Kogin
  • Tuni 'yan sanda suka isa kan titin yayin da 'yan daban suka tsere, ana cigaba da nemansu bayan kama wasu masu satar shanu 2

Kogi - Rundunar 'yan sandan jihar Kogi ta ce ta ceto wasu mutum 2 da aka yi garkuwa da su a kan babban titin Ajaokuta zuwa Itobe da ke jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan, DSP William Aya, ya sanar da hakan yayin hira da manema labarai a ranar Litinin a babban birnin jihar na Lokoja.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu
'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce sun ceto mutum biyun ne bayan 'yan sanda sun bankado wata kungiyar 'yan daba da ke addabar masu ababen hawa a kan babban titin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

"A ranar 18 ga watan Disamban 2021 wurin karfe hudu, mun samu labarin cewa 'yan daba sun rufe babbar hanyar da ke tsakanin NEPA da ASCOL ta hanyar shiga Itobe zuwa Ajaokuta inda suke ta harbe-harbe domin tsorata jama'a.
"Jami'anmu sun gaggauta daukan mataki inda suka garzaya inda lamarin ke faruwa tare da budewa 'yan daban wuta. Hakan yasa suka tsere zuwa daji, sannan aka ceto mutum biyu. Ana cigaba da kokarin damko 'yan daban," yace.

A wani cigaba makamancin haka, 'yan sandan yankin Enjema da ke karamar hukumar Kogi ta gabas sun cafke wasu mutum biyu masu suna Mohammed Alhaji da Amadu Sule Juji wadanda suka kware wurin satar shanu.

Kara karanta wannan

Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga

"'Yan sandan sun gaggauta daukan mataki bayan sun samu bayanan sirri kuma sun damke wadanda ake zargin a Ogboji da ke yankin Ankpa inda aka samu shanun sata goma sha hudu daga hannunsu.
“Za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike," Aya yace.

'Yan daba sun zagaye OAU, sun kai wa shugaban jami'a da ma'aikata farmaki

A wani labari na daban, wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki wani bangare da ke cikin jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife inda su ka kai wa shugaban jami’ar hari, Farfesa Eyitope Ogunbodede da wasu ma’aikatan jami’ar.

Matasan rike da miyagun makamai ciki har da masu bindigogi da adduna, sun dakatar da shugaban makarantar da wasu jami’ansa yayin da su ke kokarin kwace wani bangare daga jami’ar tare da harbe-harbe ko ta ina, The Nation ta ruwaito.

‘Yan daban sun kai wa jami’in hulda da jama’an jami’ar, Mr Abiodun Olanrewaju farmaki, tare da manema labarai inda su ka yi yunkurin halaka su.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: