Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto

Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar da yake sha bayan zuwa Legas a lokacin da aka kashe mutane a Sokoto
  • Malam Garba Shehu, yace ba kaddamar da littafi ya kai Buhari Legas ba, ainihin makasudin zuwansa dan jiragen ruwan sojoji ne
  • Kakakin shugaban ya kuma maida martani ga jam'iyyar PDP, wacce ta soki zuwan Buhari Legas maimakon Sokoto

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta kare ziyarar shugaba Buhari zuwa Legas a dai-dai lokacin da ake tsammanin zai je Sokoto ta'aziyyar matafiyan da aka kashe.

Fadar tace Buhari ya je Legas ne domin kaddamar da kayayyakin rundunar soji masu matukar muhimmanci waɗan da za su ƙara wa ƙasa ƙaimi wajen yaƙar yan fashin teku.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Facebook, ranar Litinin da daddare.

Kara karanta wannan

2023: Kada ku sake kuskuren amincewa da jam'iyyar PDP, Shugaban Majalisa ya roki matasan Najeriya

Garba Shehu
Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A ranar 9 ga watan Disamba, shugaba Buhari ya tafi Legas, inda ya ƙaddamar da jiragen ruwa da aka yi a Najeriya, na rundunar sojin ruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da yake martani ga masu sukar lamarin da jam'iyyar PDP, wacce ta yi zargin Buhari ya je Legas ne kaddamar da littafin Bisi Akande, Shehu yace:

"Mutanen dake cikin PDP, waɗan da ba su da wata niyya mai kyau da za su tallafa wajen inganta goben ƙasar nan, wai su suke kokarin saka ƙabilanci a ziyarar Buhari Legas."
"Saboda son rai sun zaɓi su watsar da kayayyakin da Buhari ya kaddamar, a cewar su babban dalilin zuwan sa shine kaddamar da littafi. Shin kada shugaban ƙasa ya kaddamar da jiragen ruwan sojin ruwa kwana ɗaya bayan harin (Sokoto)?"

Abinda PDP ta yi kenan tsawon lokacin mulkinta

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An maka tsohon gwamna gaban kotu kan ya ƙi neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Mista Shehu ya kara da cewa jam'iyyar PDP ta yi kokarin kawo ruɗani ta hanyar ikirarin cewa bai kamata Buhari ya je Legas ba, bisa harin da yan bindiga suka kai wani yankin ƙasa a wannan ranar.

A cewarsa wannan borin kunya ne, domin ta ya PDP zata nuna damuwa kan ayyukan yan bindiga bayan ba abin da ta iya na dakile lamarin sama da shekara 10 tana kan mulki.

Yace PDP ba ta soki shugaba Buhari kan ƙara wa rundunar soji ƙarfi ba, maimakon haka sai suka sa siyasa a cikin lamarin.

Sanarwan ta ƙara da cewa hakan ya nuna banbancin gwamnatin APC da kuma PDP, wacce ta lalata ƙasa ta hanyar wawurar dukiyar al'umma.

A wani labarin kuma Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262