Yan fashi da makami sun kai farmaki gidajen malamai na kwalejin fasaha a Ibadan
- Wasu yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun kai hari yankin gidajen malamai na kwalejin Fasaha dake Ibadan
- Kakakin kwalejin, Mista Soladoye Adewole, shine ya tabbatar da haka, yace maharan sun kai harin ne da tsakar dare
- Yace maharan sun harbi ɗaya daga cikin malamai, kuma yanzu haka yana kwance a asibiti ana kula da lafiyar sa
Kwalejin fasaha ta Ibadan ta tabbatar da kai hari Unguwar gidajen malamai da sanyin safiyar ranar litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Kwalejin ta bayyana cewa an zargin tawagar yan fashi da makami ne duka kai harin amma ba su kashe kowa ba.
Kakakin kwalejin, Mista Soladoye Adewole, shine ya tabbatar da harin a wata hirar wayar salula da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare a yankin a arewacin yankin gidajen kwalejin.
Sun jikkata malami ɗaya
Wani malamin kwalejin dake aiki da tsangayar koyar da kwas ɗin Biology, Okedara Emmanuel, wanda ya jikkata yayin harin, an garzaya da shi Asibitin jami'ar Ibadan domin kulawa da lafiyarsa.
Adewole yace babu wanda maharan suka kashe yayin da lakcaran da ya samu raunin harbin bindiga ke asibiti yana amsar kulawa ta musamman.
Vanguard ta rahoto yace:
"Babu wanda ya rasa rayuwarsa yayin harin, lakcaran da jikkata sanadiyyar harbin bindiga, an garzaya da shi asibiti domin kula da shi."
Yace tuni aka kai rahoton lamarin ga hukumar yan sanda kuma sun ɗauki matakin tsaurara tsaro a wurin da lamarin ya faru.
A wani labarin na daban kuma Mutane sun yi ta kansu yayin da Yan bindiga suka bindige Basarake har lahira a Kaduna
Kwana ɗaya bayan kashe mutum 38 a faɗin jihar Kaduna, an sake harbe basaraken gargajiya a kofar gidansa.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun harbe magajin garin Idasu, karamar hukumar Giwa, Malam Magaji Ibrahim.
Asali: Legit.ng