Da Dumi-Dumi: Mutane sun yi ta kansu yayin da Yan bindiga suka harbe Basarake a jihar Kaduna
- Kwana ɗaya bayan kashe mutum 38 a faɗin jihar Kaduna, an sake harbe basaraken gargajiya a kofar gidansa
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun harbe magajin garin Idasu, karamar hukumar Giwa, Malam Magaji Ibrahim
- Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na mutanen yankin sun tsere daga ƙauyen domin tsira
Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga sun harbe magajin garin Idasu, ƙaramar hukumar Giwa, Malam Magaji Ibrahim, har lahira.
Dailytrust ta ruwaito cewa yan ta'addan sun kashe basaraken ne awanni 24 bayan kashe mutum 38 a faɗin jihar Kaduna, ciki har da karamar hukumar Giwa.
Wani shugaban matasa a ƙauyen Rahiya, Ridwan Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa sama da kashi 70% na mutanen ƙauyen sun tsere zuwa yankunan da suka fi tsaro.
A cewarsa mazauna ƙauyen sun yi gudun hijira zuwa yankunan Zariya da kuma cikin garin Giwa, hedkwatar ƙaramar hukuma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kashe basaraken ne yayin da suka kai hari garin ranar Lahadi.
Yadda suka kashe basaraken
Wani mazaunin garin, Sharehu Idasu, yace maharan sun kashe mutumin ne yayin da ya fito daga gidansa yana kiran a kawo ɗauki garinsa.
Yace:
"An harbe shi ne yayin da yan bindiga suka shigo kauyen Idasu ranar Lahadi da daddare kuma suka sace mashina. Magajin garin ya fito domin kira a kawo ɗauki amma suka harbe shi."
Ya ƙara da cewa tuni a ka gudanar da jana'izar mamacin kamar yadda addinin musulunci ya tanazar.
Yan bindiga sun kai hari Rahiya
Wannan kisan na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyen Rahiya, karamar hukumar Giwa da yammacin ranar Asabar.
"Sama da kashi 70 cikin 100 na mutanen mu sun tsere zuwa Zariya da Giwa domin su zauna tare da wasu yan uwansu."
"Saboda abin da ya faru ya yi muni sosai, mutum 23 aka kashe a kauyen Rahiya kaɗai, 21 daga cikinsu magidanta ne, mutum biyu kacal ne ba su da aure."
Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Jalige Mohammed, bai ɗaga kiran wayan da aka masa ba domin tsokaci kan kashe basaraken.
A wani labarin na daban kuma Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasakar neman sulhu ga shugaba Buhari
Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi yankunan jihar Zamfara, Bello Turji. ya nemi a sulhu da gwamati da sarakunan gargajiya.
Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin sama da ƙasa sun ƙara ƙaimi kan yan bindiga bayan kotu ta ayyana su yan ta'adda.
Asali: Legit.ng