Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Wa Ƴan Sanda Hari, Sun Kashe Biyu Sun Cinna Wa Motarsu Wuta

Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Wa Ƴan Sanda Hari, Sun Kashe Biyu Sun Cinna Wa Motarsu Wuta

  • Wasu miyagun 'yan bindiga da ba a gano ko su wanene ba sun kai wa jami'an yan sandan Najeriya hari a yayin da suke bakin aiki a Anambra
  • Yan bindigan sun tarar da 'yan sandan ne a shingen da suka kafa a kan titi sannan suka bude musu wuta har suka kashe biyu suka kona motar yan sandan
  • Harin ya saka 'yan sandan sun tarwatse suma mutane masu ababen hawa kowa ya dare ya nemi hanya ya gudu don ya tsira da ransa da lafiya

Anambra - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a shingen yan sanda da ke kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a jihar Anambra, inda suka kashe yan sanda biyu tare da kona matarsu daya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Vanguard ta ruwaito cewa wani ganau ya ce kimanin yan sanda 10 ne ke aiki a shingen a lokacin da aka kai musu harin.

A cewar wadanda abin ya faru a gabansu, wurin ya hargitse yayin harin, hakan ya tilastawa yan sandan tsere wa nan take, suka bar wurin babu kowa.

Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sake Kai Hari, Sun Kashe Ƴan Sanda 2, Sun Cinna Wa Motocci Wuta
Yan bindiga sun kai wa yan sanda hari, sun kashe biyu sun kona motarsu. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

An kuma tattara bayanai cewa kafin afkuwar harin akwai cinkoson motocci a yankin da tsawonsa ya kai kimanin kilomita biyu.

Wanda abin ya faru a idonsu sun magantu

Wani ganau ya ce:

"Jerin gwanon motoccin ya kai mahadar Upper Iweka, duk ababen hawa sun dena motsi a hannuwan titin biyu.
"Ina cikin cinkoson motoccin kwatsam sai na ji harbin bindiga kafin ka san mai ke faruwa, kowa, har da 'yan sandan suka tsere. Sun bindige yan sanda biyu har lahira suka kona motarsu ta sintiri.

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Yi Kira Ga 'Yan Kudancin Najeriya Su Saka Baki Don Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe a Arewa

"Abin babu kyau a jiya. Ina ganin yan sandan da suka saka shingen suka nufi kai wa hari, wanda ya janyo cinkoson ababen hawa, aikin ginin titi da ake yi shima ya kara tsananta abin."

Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta bakin mai magana da yawun ta, Ikenga Tochukwu ta tabbatar da lamarin tana mai cewa an kashe jami'anta guda biyu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya ce:

"Abin da ya faru a Obasi Idemili flyover misali ne na irin sadaukarwar da jami'an yan sanda ke yi wa kasarsu da mutane baki daya.
"An yi wa mutum uku cikin yan bindigan rauni, yayin da yan sanda biyu suka rasu. Yan sandan sun kuma kwato bindigun jami'an da suka rasu. An kuma kwato mota Lexus SUV ta yan bindigan. Ana cigaba da bincike. Za mu sanar da abin da ke faruwa."

Kara karanta wannan

Sarki a arewacin Najeriya ya koka kan kwace masarautarsa da 'yan bindiga suka yi

Rundunar yan sandan ta Anambra ta ce jami'an ta za su cigaba da aiki na samar da tsaro har sa an ci galaba kan kallubalen tsaron da ake fama da shi a kasar a cewar Ikenga.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Kara karanta wannan

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164