Rashin 'Tarbiyya' Ne Yi Wa Shugaba Buhari Mummunan Addu'a, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa
- Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar NCMP a shekarar 2019, ya ce bai dace ‘yan Najeriya su dinga yi wa shugaba Buhari munanan addu’o’i ba a ranar zagayowar haihuwarsa
- Abidemi ya fadi hakan ne a Abuja ranar Litinin inda ya ce bai dace ba yadda mutane su ka dinga rubutu marasa kyau akan shugaban kasar duk da kokarinsa akan Najeriya
- A cewarsa da Buhari ya mutu a shekarun baya, da ya mutu ne a matsayin sojan da ya ke yin yaki don kare martabar kasarsa, da masu masa munanan addu’o’in sun kira shi da sadauki a yau
Abuja - Mr Ademola Abidemi, tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NCMP a zaben 2019 ya ce bai dace ba addu’o’i marasa kyau da ‘yan Najeriya su ka dinga yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar zagayowar haihuwarsa, Vanguard ta ruwaito.
Bishop Kukah: Allah bai yi kuskure ba da ya hallici mutane masu addinai da ƙabilu daban-daban a Najeriya
Abidemi ya fadi hakan ne a ranar Litinin inda ya ce bai dace mutane su dinga yi wa shugaban kasar hakan ba bayan jajircewarsa da sadaukar da kansa da ya ke ta yi don ganin kasar nan ta gyaru.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda yace bisa ruwayar Vanguard:
“Idan da shugaba Buhari ya mutu a shekarun baya lokacin yana soja yana kare martabar kasarsa, da mutane da dama sun yi masa addu’o’i tare da kiransa sadauki.
“Amma kalli yadda mutane su ka dinga rubutu marasa kan gado su na masa fatan masufu da bala’o’i su fada masa.
“Abin takaici ne ganin wannan tsana da bakin hali daga dan Najeriya zuwa dan uwansa dan Najeriya.”
Wannan ba koyarwar Bible bane
Kamar yadda ya ce, Bible bai yi koyi da hakan ba kuma yi wa wani fatan tsiya daidai ne da yin garkuwa da mutane da harkar ta’addanci.
Ya kula da yadda tsana ta sa har fatan mutuwa mutane su ka dinga yi wa Buhari, inda ya ce lallai sun cika makiyan Najeriya.
Abidemi ya kula da yadda irin mutanen nan su ka kasa yin rabin sadaukarwar da Buhari ya dinga yi tsawon rayuwarsa ga Najeriya.
Yi wa shugaban kasa fata mara kyau ba zai kawo karshen matsalolin kasa ba
Ya kara da cewa kai wa shugaban kasa farmaki da baki ba zai kawo karshen ta’addanci ba, amma ya kamata ne a dinga yi masa fatan alheri.
Abidemi ya ce Ubangiji ba ya son irin wadannan addu’o’in kuma su suke janyo wa kasa wasu masifofin saboda mutane na kara wa shugaban kasa matsaloli a kansa.
A cewarsa akwai wadanda ko haraji ba sa biya, su na lalata tituna, su na bayar da rashawa ko kuma su amsa, su cutar da mutane kuma a haka su ke yi wa shugaban kasa addu’o’i munana.
Ya kara da cewa:
“Idan ba ka bin dokokin titi ko kana kin bin dokokin kasa, bai dace ka dinga yi wa shugaban kasa fatan tsiya ba.”
Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare
A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.
Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.
Asali: Legit.ng