An titsiye ministocin Najeriya, sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi - Rahoto

An titsiye ministocin Najeriya, sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi - Rahoto

  • Ma’aikatun tarayya, bangarori da hukumomi, MDAs sun kasa bayani akan inda Naira biliyan 323.5 ta shige cikin shekarar 2019
  • Rahoton kididdiga ya bayyana yadda ma’aikatun su ka dinga saba wa dokokin biyan albashi, tare da lamushe haraji da sauran hanyoyin da kudade su ke fita
  • Ofishin kididdiga na tarayyar ya bayyana yadda hatta kudaden harajin da ma’aikatu da hukumomi su ke amsa ba su zuba su cikin asusun gwamnati

Abuja - Ma’aikatun gwamnatin tarayya da hukumomi sun kasa bayani akan naira biliyan 323.5 na 2019, yayin da aka samu ofisoshi da dama da su ka karya dokokin biyan kudi, ajiye bayanai da kuma kudaden haraji, kamar yadda rahoton kididdiga ya bayyana, Premium Times ta ruwaito.

Kashe-kashen kudaden da babu wani cikakken bayani akan su da aka samu sun hada da biyan ma’aikata kudaden alawus, kudaden kwangilar cikin ma’aikatu, biyan kudi akan ayyukan da ba a yi su ba da kuma fitar kudade babu kwakkwaran rahoto.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

An titsiye ministocin Najeriya, sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi - Rahoto
Ma'aikatu a Najeriya sun kasa bayani kan inda N324bn ya tafi, Rahoto. Hoto: Premium Times/George Ogala
Asali: Facebook

Ma’aikatu, bangarori da hukumomi (MDAs) guda ashirin da bakwai duk sun karya dokokin yayin da aka samu rauni na kula da rahotanni akan kashe-kashen kudade a akalla ma’aikatu hudu daga cikinsu, kamar yadda babban ofishin kididdiga na tarayya ya bayyana.

Mafi yawan kudi da aka kashe shi ne Naira biliyan 132.5 wanda aka yi amfani da shi wurin biyan wasu kadade ga ma’aikatan MDAs ashirin kamar yadda rahoton ya nuna.

Bangaren buga kudade na Najeriya sun kashe naira miliyan 97 ba tare da wani bayani kwakkwara ba

Bangaren buga kudi na Najeriya ya fi ko ina kashe kudi inda aka kididdiga ya kashe naira biliyan 97, yayin da hukumar ilimin kwaleji ta kasa da ke Abuja ta kashe naira miliyan biyu, wanda shi ne mafi karanci.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Kamar yadda ofishin kididdigar ya bayyana, kashe-kashen kudin ya saba wa sakin layi na 415 na dokar kudi wacce ta ce:

“Gwamnatin tarayya tana bukatar bayanai dangane da ko wanne kudi da ya shiga ko ya fita daga asusunta. Kada a kuskura a kashe kudade ba tare da wani dalili ba.”

Premium Times ta rahoto dayan babbar asarar kudi da rahoton ya nuna na naira biliyan 127.1, na kudaden haraji da aka samu a cikin ma’aikatun wadanda MDAs 15 ba su lissafa da su ba.

A karkashin dokokin gwamnati, wajibi ne duk wasu hukumomin gwamnatin tarayya wadanda aka biya isassun kudaden da su dinga tura kudaden harajin da su ka samu zuwa asusun gwamnatin tarayya.

A 2011 an fitar da wata takarda wacce ta bukaci ko wacce hukuma da ta yi amfani da a kalla kaso 75 bisa dari na kudaden harajinta don tafiyar da ayyuka, sannan ta dinga tura kaso 25 zuwa asusun gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya aminta a biya likitoci albashinsu da aka rike lokacin yajin aiki

Hukumar kwastom ta wawuri kudade masu yawan gaske

A cikin naira biliyan 127.1 da ba a shigar dasu ba cikin asusun gwamnati, hukumar kwastom ta kasa ce ta fi ko wanne bangare lamushe kudi na naira biliyan 125, yayin da hukumar ci gaban rafin Anambra-Imo ta ci mafi karancin kudi na naira miliyan 5.

Sannan kuma MDAs tara sun kashe naira miliyan 49.5 a kan abubuwan da babu su cikin kasafi, yayin da ma’aikatar noma da bunkasa karkara ta fi ko wacce ma’aikata lamushe kudi, naira biliyan 48, sai kuma hukumar hada magunguna ta kasa da ke Abuja ta zama mafi karanci, inda ta kashe Naira miliyan daya.

MDAs goma sun kashe wata naira biliyan 18.2, inda ma’aikatar noma har ila yau ta fi ko wacce ma’aikata kashe kudi, na naira biliyan goma sha daya.

Rahoton ya nuna yadda aka biya wasu MDAs din naira biliyan 6.5 ba tare da rubutacciyar takarda ba, wanda cikin ma’aikatun hudu ma’aikatar lafiya ta tarayya da ke Keffi ta fi ko wacce wawushe kudin inda aka biya ta naira biliyan biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164