Gwamna ya sanar da lokacin da zai fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addancin jiharsa
- Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sanar da cewa zai fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa a watan Janairun shekara mai zuwa
- A cewar gwamnan, jami'an tsaro sun yi ram da mutum 18 da ake zargi kuma da kansu suka bayyana wadanda ke daukar nauyin rikicin jihar
- Uzodinma ya kara da cewa, jami'an tsaro sun kara bincike kuma an gano asusun bankin da ke tura wa miyagu kudi, hakan ne ya zama babbar shaidar gwamnati
Imo - Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo, ya ce zai fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a jihar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da ya ke jawabi ga sabbin shugabannin jam'iyyar APC da aka zaba, TheCable ta ruwaito.
The Nation ta ruwaito cewa, ya ce jami'an tsaro sun yi ram da wadanda ake zargi 18 kuma sun fallasa sunayen wadanda ke daukar nauyin ta'addancin da ake yi a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Uzodinma ya kara da cewa, zai fallasa wadannan sunayen yayin taro da masu ruwa da tsaki a Imo wanda za su yi a ranar 3 ga watan Janairun 2022.
"Dukkan mutanen da aka yi haya su kashe mutane na, mun fara daukar su daya bayan daya. A yanzu haka muna da mutum 18 da ake zargi.
Wasu daga cikinsu sun bayyana sunayen wadanda ke biyansu," yace.
"Mun samu bayanan asusun bankin da ake turo musu kudi kuma muna da shaida. A ranar 3 ga watan Janairun 2022, zan yi jawabi ga masu ruwa da tsaki kuma zan bayyana sunayen su daya bayan daya."
Yankin kudu maso gabas na kasar nan ta na fuskantar hare-hare a cikin lokutan nan, inda jihar Imo ta ke kan gaba wurin samun yawan hare-hare.
Jihar ta dinga fuskantar barazanar 'yan awaren IPOB, lamarin da ya kawo gurguncewar kasuwanci.
A watan Mayu, gwamnan ya ce nan babu dadewa za a tsamo masu assasa rikici a jihar.
Gwamnan ya dora laifin rikicin kan fusatattun 'yan siyasa inda ya kara da cewa masu daukar nauyin rigingimun suna hassada da shekara daya da ya yi bisa karagar mulkin jihar.
An sake samun gawar wani basarake da aka sace a Imo
A wani labari na daban, jama'ar yankin Ihitte Ihube da ke karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo sun shiga cikin jimami da dimuwa bayan samun gawar basarake Eze Pau Ogbu da aka yi.
A ranar Lahadi, an sace Eze Ogbu da wani shugaban matasa an sace su bayan an kone fadarsa da wasu ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Amma an samo gawarsa a ranar Laraba kuma an aika da ita fadarsa yayin da ake shirin birne shi, SaharReporters ta ruwaito.
Asali: Legit.ng