Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a

Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a

  • Miyagun mayakan ta'addanci na Boko Haram sun kai mummunan farmaki kauyen Kilangal da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno
  • 'Yan ta'addan an gano sun halaka wasu mutane masu tarin yawa sannan wasu sun jigata yayin da suka banka wa wasu gidaje wuta
  • Bayan sa'o'i biyu, jiragen yakin sojin saman Najeriya sun bayyana domin kai dauki, amma tuni 'yan ta'addan suka gama barnarsu tare da komawa daji

Askira Uba, Borno - Akwai yuwuwar mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunika yayin da mayakan ta'addancin Boko Haram suka kai farmaki karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan suna dira kauyen Kilangal, asalin garin su Injiniya Abdullahi Musa Askira, mataimakin kakakin majalisar jihar Borno a ranar Lahadi, kuma sun banka wa gidaje wuta.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a
Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jiragen NAF sun kai dauki

Kamar yadda wata majiya ta sanar, jiragen yakin sojoji sun bayyana bayan sa'o'i 2 amma tuni 'yan ta'addan sun riga da sun yi barna, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun yi barna ba tare da tsayawa ba inda daga bisani suka fada daji kuma suka bar wasu matattu," majiyar tace.

Rahoto: Yadda rashin tsaro ya halaka 'yan sandan Najeriya 322, sojoji 642 a shekara 1

A wani labari na daban, lamari mai kama da bikin zubar da jini ya auku a kasar nan inda aka halaka fiye da ‘yan sanda da sojoji 964 yayin mayar da hare-hare cikin shekara daya, kanar yadda binciken sirrin SB Morgan su ka ruwaito.

Rahoton wanda ma’aikatar binciken sirrin ta gudanar a ranar Alhamis ta gano yadda kisan ya auku tsakanin watanni ukun kashen shekarar 2020 da watanni taran farkon shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

A cikin ‘yan shekarun nan, rashin tsaro ya nunku a bangarori daban-daban na kasar nan. An samu matsaloli irin na garkuwa da mutane, ta’addanci, fashi da makamai, rikicin manoma da makiyaya da sauransu.

Don kawo karshen wadannan matsaloli, sojojin kasar nan yanzu sun ja ragamar tsaro a yankuna daban-daban na kasar nan musamman a arewacin Najeriya.

Yayin tsokaci akan matsalar tsaro, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin jawabinsa na ranar bikin ‘yancin kai, ya ce a watannin da suka gabata bangarori daban-daban na kasar nan sun jigata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng