Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su
- Gwamna Uzodimma na jihar Imo ya ce yanzu haka yana da sunayen wadanda ke haddasa rashin tsaro a jiharsa
- Gwamnan ya ce zai bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addancin a cikin Janairun 2022 mai zuwa
- Uzodimma ya sha alwashin cewa duk wanda ke da hannu a aikata laifi za a hukunta shi, komai girmansa
Owerri, Imo – Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da za a gudanar a ranar Litinin 3 ga watan Janairu, 2022.
Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, sun bayyana sunayen wadanda suke haddasa rashin tsaro, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Legit.ng ta tattaro cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a garin Owerri a lokacin da yake jawabi ga zababbun jami’an jam’iyyar APC.
Ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya don tabbatar da cewa jihar ta zauna lafiya.
Gwamna Uzodimma ya kara da cewa duk wanda ke karfafa aikata laifuka a jihar, komai girmansa, to zai fuskanci fushin doka.
Kalamansa:
“Bari in bayyana cewa, an kashe wadannan kansiloli biyu kwanan nan, kuma an kama wadanda suka kashe su kuma sun amsa abin da suka aikata.
“Kada ku ji tsoro. Idan har nine Gwamna a jihar nan, za su fuskanci fushindoka. Muna da shaida kan wadanda ke da hannu a lamarin rashin tsaro bisa bayanan da aka samu daga wadanda ake zargi.
"Zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2022, lokacin da zan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na Imo, zan fitar da sunayensu daya bayan daya tare da shaidar rawar da suka taka."
Gwamnati ta tona asirin kungiyoyin da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
A baya kadan, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd), ya bayyana sunayen kungiyon da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya da sauran kasashen Sahel.
A cewarsa, Jama'at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS sune kunyoyin da ke karfafa ayyukan ta'addanci, The Nation ta ruwaito.
Munguno ya bukaci masu wa'azin addinin Islama da Limamai da su dauki matsaya mai kyau don tallafawa ayyukan gwamnati a yaki da ta'addanci.
Asali: Legit.ng