Bukola Saraki ya cika wa mahaifinsa alkawarin gina katafaren masallaci, 'yan Najeriya sun yi martani
- An yiwa tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da addu’o'i da yabo yayin da ya gina masallaci a birnin Ilorin
- Saraki ya ce ya gina masallacin ne domin cika alkawarin da ya yi wa mahaifinsa, Oloye Olushola Saraki
- ‘Yan Najeriya da dama da suka hada da mai taimaka wa Shugaba Buhari, Bashir Ahmad, sun yi wa Saraki addu’ar alheri
Ilorin, Kwara - A jiya Asabar ne tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya bayyana wani kyakkyawan aikin da ya yi.
A cikin rubutun da ya yada a shafinsa na Facebook, Saraki ya bayyana cewa ya gina wani katafaren masallaci a garin Ilorin don cika alkawari.
A cewarsa, tun farko ya dauka wa mahaifinsa alkawarin gina masallaci, amma bai samu ya cika ba har sai da mahaifin nasa ya rasu.
A kalaman Saraki, cewa yayi:A kalaman Saraki, cewa yayi:
"Na yi godiya ga Allah!
"Kafin rasuwar mahaifina, Oloye na yi masa alƙawarin zan gina sabon masallaci kusa da gidanmu dake Agbaji.
"Allah bai bani ikon aikata hakan a yayin da mahaifin nawa yake raye ba.
"Duk da haka, a yau, domin cika alƙawarin da na yi wa marigayi mahaifina, na yi tarayya wurin buɗe masallacin da na gina, wanda aka ɗauki lokaci ana aikinsa.
"Ina addu'ar Allah Ya amshi salloli da addu'o'in da za a gabatar a wannan masallaci. Aameen."
Martanin 'yan NajeriyaMartanin 'yan Najeriya
Baya ga yada wannan kyakkyawan aikin, mabiya shafinsa na Facebook sun yi martani, inda suka yi masa addu'o'in alheri.
Daga cikin wadanda suka masa addu'a, akwai wani hadimin Buhari kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad.
Bashir Ahmad ya bayyana haka a shafin Facebook cewa:
"Masha Allah. Allah ya saka da alkhairi."
Usman M. Isah yace:
"Allah Ya cika maka lada, Ya Kai rahama kabarin Mahaifin ka Ya sa bayan ka tayi kyau. Muna fatan yin tarayya da kai wajen Gina al'umma."
Fatee Fateemah ta tofa nata addu'an:
"Abubakar Bukola Saraki Allah ya jadadda rahama ga iyayen mu da suka riga mu gidan gaskiya. Allah ya bada ladan gina Masallaci."
Nura Sirajo shi kuwa ya yiwa mahaifin Saraki addu'a da cewa:
"Allah ya jikan Dr Saraki (Leader) Allah yasa yana Aljanna, Allah ya baka ikon yin aiki na Alkairi irin nashi."
Abubakar Ibrahim Zakiru shi kuwa bayyana tsokaci yayi, inda yace:
"Masha Allah yasa karkaba Yan izalah wlh inkabasu gobe iyayen naka zasu zaga acikin Allah yasaka Maka da Alkhairi yasa yazama sadaqatur jariya agareshi."
Abba Musa Zango Gwarzo yace:
"Masha Allah. Allah yasaka maka da Alkhairi
"Allah yakai ladan Kabarin mahaifin ka yadda ka gina dakin Allah Kaima Allah ya ginawa mahaifin ka gida A aljanna ameen."
Cocin Katolika ya gina wa musulmai masallaci a jihar Adamawa
A wani labarin, Bishop na cocin Katolika na Yola, Revd. Fr. Stephen Mamza, ya bayyana cewa ya gamu da adawa lokacin da ya bayyana aniyarsa ta gina masallaci ga Musulmai 'Yan Gudun Hijira a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Mamza, wanda ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Punch, ya ce da farko, ba su nuna wariya ga kowa ba lokacin da shi da sauran mambobin cocin suka dauki bakuncin 'yan gudun hijira.
Legit.ng ta tattaro cewa malamin ya ce ba su tambayi addinin da ‘yan gudun hijirar ke bi ba ko kuma su nemi cocinsu da suke bauta, ya kara da cewa an dauki 'yan gudun hijirar a matsayin ’yan Adam da ke bukatar taimako.
Asali: Legit.ng