Makudan miliyoyi da abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sarauniyar kyau ta Najeriya, Shatu Garko
- Tun bayan sanar da sarauniyar kyau ta wannan shekara, an shiga mamakin yadda wata matashiya ta lashe gasar kyau
- Kasancewar ta bahaushiya mai sanya Hijabi, hakan ya jawo cece-kuce a wasu bangarorin kasar nan musamman Arewa
- A wannan rahoton, an tattaro wasu kadan daga cikin bayanan wannan baiwar Allah da ta ciri tuta a gasar Miss Nigeria
Kano - A jiya Asabar ne labari ya karade kafafen watsa labaran Najeriya kan sanar da wata 'yar jihar Kano, Shatu Garko a matsayin sarauniyar kyau ta Najeriya.
Shatu Garko ‘yar shekaru 18 da haifuwa da ake kallo da Hijabi ta ciri tuta a gasar kyau ta Miss Nigeria karo na 44 wannan shekara ta 2021.
An nada ta a matsayin sarauniya ta 44 ne a gasar a lokacin tantacewar karshe na gasar da aka gudanar a Legas a daren Juma’a, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Jaridar Punch ta ba da kadan daga bayan Shato Garko, inda ta bayyana wasu abubuwa biyar akanta.
A kasa mun tattaro muku kadan daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani game da Shatu Garko
1. Shatu Garko ‘yar jihar Kano ce.
2. Ta kasance shahararriya a Instagram tun ma kafin ta shiga gasar kyau ta Miss Nigeria.
3. Duk da kasancewarta matashiya daga cikin wadanda suka shiga gasar, Garko ya doke wasu 17 inda ta zama misali na farko mai saka hijabi da ta ci kambin Miss Nigeria.
4. Garko, baya ga kasancewaeta samfurin kwaikwayo a shafukan sada zumunta, tana son hawan dawakai da wasan kwallon kwando.
5. A matsayin Miss Nigeria na 44, Garko ta tafi gida da garabasar Naira miliyan 10, sabuwar mota, zama na shekara guda a wani katafaren gida da dai sauransu.
Kyakkyawar budurwa 'yar Kano ya ciri tuta
A tun farko, kyakkyawar budurwa 'yar Arewa maso yammacin Najeriya, Shatu Garko, ta lashe gasar Mace mafi kyau a Najeriya watau 'Miss Nigeria' na shekarar 2021.
Shatu Garko, yar shekaru 18 kacal ce mace mai Hijabi daya tilo cikin dukka sauran yan takaran gasar.
Adebimpe Olajiga ta bayyana hotunan bikin yayinda ake karrama Shatu bayan nasarar da tayi a gasar.
Asali: Legit.ng