Sokoto: Tambuwal ya ɗauki mataki kan mawaƙin da ya gwangwaje shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, da waƙar yabo
- Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal ya bada umurnin a kama mawakin da ya fitar da waka inda ya rika yabo da jinjina ga shugaban yan bindiga
- Gwamnan ya dauki wannan matakin ne kwanaki uku bayan faifan wakar ya bazu a dandalin sada zumunta kuma mutane suka fara maganganu a kan wakar
- Sai dai duk da haka, wakar da aka yi na yabon shugaban yan bindiga, Bello Turji, yana nan yana bazuwa a arewacin Najeriya, a yayin da mutane da dama ke fushi da hakan
Jihar Sokoto - A ranar Juma'a, 17 ga watan Disamba, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya bada umurnin a kamo mawaki, Muhammad Danshanawa saboda yabon shugaban yan bindiga, Bello Turji, a wakarsa.
A cikin kalaman da ke cikin wakar, Danshawa ya yabi dan ta'addan, Turji, inda ya kira shi zaki, jan namiji kuma babban jagora mai kwarjini.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sahara Reporters ta nuna cewa umurnin gwamnan na zuwa ne kwanaki uku bayan wakar ta bazu a kafafen sada zumunta daban-daban.
Da ya ke magana a kan wakar, Gwamna Tambuwal ya ce:
"Mu bada umurnin a kama shi saboda ya zama darasi ga wasu.
"Hakan na cikin dalilan da yasa na shawarci Shugaban Kasa, Babban kwamandan hafsoshin Najeriya ya duba yiwuwar bada horaswa na bindiga ga mutanen yankunan da suka fama da kallubalen tsaro."
Martanin mutane
A cewar Sahara Reporters, wasu mazauna garin Sokoto wanda suka yi tir da wakar sun bayyana cewa abin da mawakin da ya yi rashin kishin kasa ne.
Sqaudron leader, Aminu Bala, ya ce:
"Wannan wakar na iya kangarar da matasa su fara sha'awar ko kwaikwayon 'yan ta'addan."
Wani mutum mazaunin arewacin Najeriya, Abdullahi Bala ya ce:
"Wannan abin bakin ciki ne; kuma yana zuwa a lokacin da ake fama da mummunan kallubalen tsaro. A halin yanzu, mutane ba su iya zuwa Sokoto zuwa Illeila, amma wani na wakar yabon yan ta'adda."
Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto
A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.
Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.
Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.
Asali: Legit.ng