Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Ilimi dai kogi ne kamar yadda masu iya magana kan ce kuma kowa akwai iya basira da hazaka da Allah ya bashi a bangarori na rayuwa daban-daban har ma da harkar karatu.
Wadannan daliban sun shiga jami'a ne ba tare da sakamako na a zo a gani ba amma daga bisani suka fita da sakamakon da ya zama abin yabo.
A wannan rahoton, Legit.ng ta haskaka tauraronta kan wasu daliban Najeriya 4 da suka yi bajinta a makarantunsu ta hanyar karyaa tarihin da ake ganin ba masu yiwuwa bane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Fetimi Balogun Bebetebe
Fetimi Balogun Bebetebe ya karya wani tarihi na tsawon shekara 55 da Jami'ar Cebu da ke kasar Philippines.
Matashin wanda gwamnatin tarayyar Najariya ta dauki nauyin karatunsa na digiri a bangaren injiya na jiragen ruwa a karkashin hukumar kula da sifirin jiragen ruwan Najeriya, NIMASA, ya samu sakamako mafi daraja a jami'ar ta kasar waje.
2. Otoko Steven Edwards
Otoko Steven Edwards ya fara nuna bajintarsa ne a Jami'ar Jihar Rivers inda ya kammala digirinsa da makin CGPA 5.0.
Matashin ya yi digirinsa na farko ne a tsangayar koyar da lissafi, inda ya karya tarihin da aka kafa tsawon shekaru 41 a tarihin Jami'ar.
Ya sauya ne daga tsangayar karatun injiniya zuwa lissafi bayan ya gano ya fi kaunar lambobi a kan injina.
3. Mbagwu Johnpaul Chiagoziem
A Jami'ar Jihar Imo, Owerri, matashi Mbagwu Johnpaul Chiagoziem ya kafa tarihi bayan ya kammala digiri sa sakamako mafi daraja na 1st Class a 'Industrial Physics' a karon farko bayan shekaru 39.
Bajintar da ya yi ya saka mutane da dama sun yi alkawarin za su bashi tallafin kudade amma watanni 8 bayan babu ko daya cikinsu da ya cika alkawarin.
4. Ruqayyah Adelakin
Matashiya, Ruqayyah Adelakin, ce ta karya tarihi na shekaru 19 a Jami'ar Ladoke Akintola ta Fasaha, LAUTECH.
Ruqayyah, wacce ta kammala digiri a bangaren 'Biochemistry' ta ce da farko ba wannan makarantar ta ke son zuwa ba amma ta samu gurbin karatu kuma ta amince ta fara a maimakon zaman gida.
Asali: Legit.ng