An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

  • Wasu miyagu da a tabbatar ko su wanene ba sun halaka a wani Mr Enogu da 'ya'yansa biyu Chigbo Enogu da Sundaya Enogu
  • An kashe su ne a yayin da suke hanyar komawa gidansu a hanyar Ore Egbebe a karamar hukumar Ado bayan kammala aiki a gona
  • Shugaban karamar hukumar Ado, James Oche, ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma ce yan sanda sun kama wasu sannan ana zurafa bincike

Benue - Wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Na Kaduna, Wani Ɗan Majalisar Da Ƴan Bindiga Suka Harba Ya Mutu

An halaka maihaifi ya 'ya'yansa 2 a hanyarsu ta dawowa daga gona
An kashe magidanci da 'ya'yansa biyu a hanyarsu ta dawowa daga gona. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Mazauna kauyen sun ce marigayin da yaransu sun tafi gonarsu ne inda aka kai musu hari aka halaka su a hanyar dawowa gida bayan kammala aikin ranar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban karamar hukuma ya tabbatar da afkuwar lamarin

James Oche, shugaban karamar hukumar Ado, ya tabbatarwa manema labarai afkuwar lamarin a Makurdi yana mai cewa ya yi bakin cikin samun labarin kisar da aka yi wa mutanen uku.

Oche ya ce tuni an sanar da jami'an tsaro kuma tuni sun fara bincike da kan lamarin har ma an kama wasu mutane kadan da ake zargi kuma suna taimakawa wurin cigaba da binciken.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Shugaban karamar hukumar, ya yi kira ga al'ummar yankin su cigaba da zama lafiya da juna tare da bin doka da oda, ya basu tabbacin gwamnatinsa a kullum tana kokarin kiyaye rayuka da dukiyoyin 'yan Ado.

Hakazalika, Kakakin yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ita ma ta tabbatar da afkuwar lamarin.

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164