Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023

Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023

  • Babban zaɓen 2023 na kara kusantowa yayin da matsalar tsaro ke kara taɓarɓarewa a Najeriya
  • Tsohon shugaban INEC, Farfesa Jega, ya bayyana cewa wannan matsalar zata iya hana gudanar da zaɓe a shekarar 2023
  • Jega yace wajibi a tunkari tsaron kasar nan dagaske, idan kuma ba haka ba babu jam'iyyar da zata amince da zaɓen

Ibadan - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargaɗin cewa matukar ba'a shawo kan matsalar tsaro ba, babban zaben 2023 ba zai yuwu ba.

Jega ya yi wannan furucin ranar Alhamis a Ibadan, yayin da yake jawabi na musamman a wurin bikin cikar tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi, shekara 72, wanda ya gudana a jami'ar Ibadan.

Punch ta rahoto Jega na ƙara jaddada cewa tsaro babban jigo ne na kowane irin zaɓe, matukar ana son kowace jam'iyya ta amince da sakamakon wannan zaben.

Kara karanta wannan

Yan majalisa sun amince Buhari ya sake karban bashin $5.8bn, abubuwa 4 da za'ayi da su

Attahiru Jega
Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, Ya faɗi babban matsalar da zata hana zaben 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa, matsalar tsaro dake ƙara mamaye ƙasar nan wani babban barazana ce ga shirin gudanar da zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me rashin tsaro zai haifar wa zabe?

Jega, wanda kwararre ne a ilimin kimiyyar siyasa, yace wajibe ne a magance duk wani ƙalubalen tsaro domin tabbatar da zaɓe mai zuwa.

Jega yace:

"Har sai an gudanar da zaɓe a wuri mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan ba haka ba gaskiya da kuma sahihancin sakamakon zaɓen zai zama abin tantama."
"Shi kalubalen tsaro yana rushe ingancin zaɓe ne baki ɗaya. Kuma yana lalata duk wani shiri na gudanar da zaɓen ya hana yin zaɓen.
"Matsalar tsaro zata sanya babu wanda zai kalli sakamakon zaɓen da mutunci balle ya amince da shi."

Daga nan kuma, Jega ya kara da gargaɗin cewa yayin da zaben ke kara kusantowa ne ƙalubalen tsaro ke ƙara yawaita, kuma hakan babbar barzana ce.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya yi magana kan rashin tsaro karkashin mulkin Buhari

A wani labarin kuma Sanata ya roki Mala Buni ya ɗage gangamin taron APC na kasa, ya faɗi dalilai

A ranar Alhamis, sanata Orji Uzor Kalu, ya roki kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, Gwamna Mala Buni, da mambobin kwamitin shirye-shirye su ɗage babban taron jam'iyya na ƙasa wanda za'a gudanar a watan Fabrairu.

A wasikar da ya aike wa Mala Buni, Kalu ya roki jagororin APC su gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa da shugabannin APC na ƙasa lokaci daban-daban a wurin taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262