Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa
- An sake samun afkuwar wani harin 'yan bindiga a jihar Kaduna, lamarin da ya kai ga hallaka wani mutum
- Rahotanni sun bayyana cewa, an kuma sace 'ya'yan mutumin su uku a daren jiya Laraba 15 ga watan Disamba
- Daga makon jiya zuwa wannan makon an samu munanan hare-hare a jihar Kaduna, musamman a Zariya
Zariya, Kaduna - Daily Trust ta rahoto cewa, wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe wani Alhaji Habibu na yankin Sayen Lenu a Dutsen Abba na karamar hukumar Zariya a Kaduna tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa uku.
Sayen lemu wani kauye ne da ke kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya, kuma yana da tazarar kilomita 5 daga inda ‘yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Litinin.
Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun isa gidansa da misalin karfe 11 na daren Laraba inda suka harbe shi har lahira sannan suka yi awon gaba da ‘ya’yansa uku.
Majiyar ta shaida cewa:
“Ba mu tunanin an turo a kashe shi ne. Mun yi imanin cewa suna cikin ‘yan bindigan da ke ta’addanci a yankin a baya-bayan nan."
"Kun san wannan yanki yana da yawan samun hare-hare daga 'yan bindiga a cikin shekara guda, amma duk da haka ba a dauki matakin ceto rayukanmu daga hare-haren da suke kai wa ba."
Idan baku manta ba, a ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane biyar a yankin Dallatu da Kasuwar Da’a da ke Dutsen Abba a Zariya.
Lamarin ya faru ne sa’o’i 24 bayan ‘yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da kashe mutane uku da yin awon gaba da mutane da dama, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigan da suka kai farmaki kauyen Dallatu da misalin karfe 1 na safiyar ranar Laraba, sun yi garkuwa da mutane biyu tare da zarce wa zuwa kauyen Kasuwar Da’a inda suka yi awon gaba da wasu mutum shida daga cikinsu akwai yara uku.
Sai dai majiya ta shaida cewa an sako yaran uku da safiyar Laraba, inda sauran biyar ke hannun 'yan ta'addan.
Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika
A wani labarin, wasu daga cikin yan bindigan da suka kashe masallata 18 a kauyen Maza-Kuka, karamar hukumar Mashegu, jihar Neja, sun shiga hannu.
Kwamishinan kananan hukumomi, cigaban karkara, harkokin nade-nade da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, shi ne ya sanar da haka yayin da yake bayani ga manema labarai a Minna ranar Laraba.
Daily Trust ta ruwaito kwamishinan na cewa ba zai iya bayyana adadin waɗan da suka shiga hannu ba a halin yanzu.
Asali: Legit.ng