Da Dumi-Dumi: Adebanjo ya bukaci EFCC ta binciki dukiyar Bola Tinubu da Bisi Akande
- Shugaban kungiyar Afenifere, ya maida martani ga Bisi Akande, kuma ya bukaci ya fito ya bayyan hanyar da ya samu dukiyarsa
- Adebanjo ya kuma kalubanci jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, ya faɗi yadda ya tara dukiya kuma ya bar EFCC ta yi aikinta a kansa
- Wannan na zuwa ne bayan Bisi Akande, ya zargi cewa Adebanjo ya matsa wa Tinubu a baya har ya gina masa gida a Lekki
Lagos - Shugaban kungiyar yarbawa, Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, ya caccaki tsohon shugaban APC, Bisi Akande, kan cewa ya roki jagoran APC, Bola Tinubu, ya gina masa gida a Lekki.
Punch ta rahoto cewa shugaban Afenifere, ɗan kimanin shekara 93 ya bayyana yadda ya tara kudinsa har ya gina gidan wanda yake zaune a ciki yanzu haka.
Adebanjo ya bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gudanar da bincike kan hanyoyin samun kudin Tinubu da Akande.
Mista Adebanjo ya yi wannan furuci ne a wurin taron manema labarai a Legas, ranar Alhamis, a wani martani ga zargin da Bisi Akande ya masa a cikin litafinsa mai fegi 559.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kaddamar da litattafin, wanda aka raɗa wa suna, "My Participations" ya gudana a Legas, kuma ya samu halartan jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu.
A cikin littafin, Akande ya bayyana yadda shugaban Afenifere ya roki Bola Tinubu ya gina masa gida a Lekki, kuma gidan ne yake zaune a ciki.
Martanin Adebanjo ga Akande
Da yake martani kan zargin da aka masa, Adebanjo yace yana mamakin yadda har yanzun Tinubu bai maida wa Akande martani ba duk da cewa tsohon gwamnan ya yabe shi (Adebanjo), da rashin karban rashawa.
Daily Trust ta rahoto ya cigaba da cewa:
"An faɗi abubuwa da dama a jaridu da kafafen sada zumunta dan a bata mun suna, amma na yi wa kaina alkawarin maida martani kan karyar cewa Bola Tinubu ne ya gina mun gida a Lekki.
"Ko kaɗan maganar ba gaskiya bane, ni na gina gida a Lekki da kuɗi na, ta hanyar siyar da wasu kadarori na uku, bashin dana ƙarba daga bankin GT, da kuma siyar da wasu kadarori da tsohon shugaba Obafemi Awolowo ya ba ni."
Daga nan kuma Adebanjo ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya siyar da kadarorin da kuma yadda ya samu bashi daga GT har ya gina gidansa. Ya kuma bukaci EFCC ta yi bincike dan tabbatar da haka.
Ina kalubalantar Akande da Tinubu - Adebanjo
Shugaban Afenifere ya ƙara da cewa:
"Ina ƙalubalantar Bisi Akande, ya fito ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya mallaki dukiyarsa, kamar yadda na yi a yanzun."
"Haka nan Bola Tinubu, ya fito ya yi bayani kan hanyoyin da yabi ya tara dukiyarsa, wacce ya yi amfani da ita wajen neman zaɓen APC a kudu ta yamma da zaɓen shugaba Buhari."
"Kuma ya baiwa hukumar EFCC dama ta tabbatar da abinda ya faɗa kamar yadda ni na yi yanzu."
A wani labarin na daban kuma Jami'an DSS da Yan Sanda sun rufe cibiyar Press Centre a jihar Kano
Jami'an hukumar tsaro ta DSS, jami'an yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun rufe sakateriyar kungiyar yan jarida (NUJ) wacce aka fi sani da Press Center a jihar Kano.
Wan nan ya faru ne bayan wata ƙungiya ta bayyana shirinta na amfani da Press Center a matsayin wurin da zata gudanar da zanga-zangan lumana kan tabarbarewar tsaro a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng