Yanzu-Yanzu: Jami'an DSS da Yan Sanda sun garkame Press Center a Kano
- Hukumomin tsaro da suka haɗa da yan sanda, DSS da sauransu, sun rufe sakateriyar NUJ (Press Centre) a jihar Kano
- Jami'an sun ɗauki wannan matakin bayan gano ana shirin amfani da wurin domin gudanar da zanga-zangan lumana
- Shugaban NUJ na jihar Kano, Abbas Ibrahim, yace kungiyarsu ba ta da masaniya kuma ba ta baiwa kowa dama ba
Kano - Jami'an hukumar tsaro ta DSS, jami'an yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun rufe sakateriyar kungiyar yan jarida (NUJ) wacce aka fi sani da Press Center a jihar Kano.
Wannan ya faru ne bayan wata ƙungiya ta bayyana shirinta na amfani da Press Center a matsayin wurin da zata gudanar da zanga-zangan lumana kan tabarbarewar tsaro a ƙasar nan.
Daily Trust ta rahoto cewa waɗan da suka shirya zanga-zangan sun rubuta a shafin sada zumunta domin gayyatar mutane.
Sai dai zanga-zangan ba ta yuwu ba, domin yadda aka girke motocin hukumomin tsaro ɗauke da jami'ai, kuma wasu na sintiri a baki ɗaya ilahirin kewayen wurin, yayin da kofar shiga take a kulle.
Da yake jawabi a kusa da cibiyar, Barista Abba Hikima, ɗaya daga cikin waɗan da suka shirya zanga-zangan, yace:
"Dalilin da yasa muka shirya wannan zanga-zanga shi ne dan mu nuna fushin mu kan abinda ke faruwa da kuma yadda abubuwa ke wakana a ƙasar nan."
"Duk wani ɗan Najeriya ko daga wani yanki ya fito yasan yadda tsaron ƙasar ya tabarbare, kuma mutane sun san ba wanda ke iya bacci hankali kwance, ga shi ba abinda ake yi a kai."
"Shugabannin mu ba su damu da halin da muke ciki ba, sun fi damuwa da kaddamar da littafi. Shiyasa muka fito mu yi kira ga gwamnati, mune muka tura su madafun iko, kamata ya yi su mana abinda muke so.
Shin NUJ ta san da faruwar lamarin?
Da yake martani kan lamarin, shugaban NUJ na Kano, Abbas Ibrahim, yace basu da masaniya kan shirin gudanar da zanga-zangan.
Ya ƙara da cewa babu wanda suka baiwa damar amfani da Press Centre a matsayin wurin haɗuwa da fara zanga-zanga.
Vanguard ta rahoto yace:
"Abin da muka sani shi ne wata kungiya mai suna haɗakar kungiyoyin arewa ta sanar da mu cewa zasu gudanar da taron manema labarai wanda zasu yi amfani da Press Centre."
"Amma da muka gano ɓoyayyar manufarsu jiya da yamma, sai muka fasa ba su damar amfani da wurin, kuma muka sanar musu, su nemi wani wurin. Babu wanda muka ba umarnin ya zo nan ya yi zanga-zanga."
A wani labarin kuma Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya
A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.
Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.
Asali: Legit.ng