Ya zama dole Kirista ya gaji Shugaba Buhari a 2023, Cocin PFN
- Shugaban Cocin PFN ya bayyana bukatar miliyoyin mabiyansa dake fadin Najeriya a shekarae 2023
- Bishop Oke ya bayyana cewa rashin adalci ne idan ba'a bari Kirista ya gaji shugaba Buhari ba idan wa'adinsa ya kare
- Malamin addinin ya bayyana cewa sam ba zasu yarda wata jam'iyya ta zabi Musulmai matsayin yan takara ba
Ibadan - Shugaban PFN ya yi kira ga yan Najeriya cewa kasar nan ta kowa ce kuma wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya bari Kirista ya gajeshi.
A cewarsa, shaidanin mutum ne kawai zai yi kokarin kakaba musu dan takara Musulmi.
Shugaban mai suna Bishop Wale Oke, ya bayyana hakan a taron gangamin Zoe World Congress da ya gudana a Jami'ar Ibadan ranar Litinin, rahoton Sun.
Yace:
"Abinda muke so shine Shugaban kasa Kirista. Wajibi ne Buhari ya mika mulki wa Kirista. Kowa ya sani cewa duk wani sabanin haka ba zamu yarda ba. Mambobin cocin PFN milyan 65 ba zasu amince ba."
"Najeriya ta dukkanmu ce, za'a samu nasara ne kawai idan akayi adalci da daidaito."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abinda muke kira ga ayi kenan. Idan manyan jam'iyyun biyu suka zabi yan takara Musulmi da Musulmi, zasu sha kasa."
Ikon Allah kadai zai wanye kan Najeriya, ba shirin wani shaidanin barawo, mara kishi kuma shaidanin dan siyasa dake ganin yana da kudin saye jama'ar kudu maso yamma da Najeriya ba."
Ba fa zamu yarda Musulmi da Musulmi su yi takara a zaben 2023 ba, Cocin PFN
Kungiyar mabiya cocin Pentecostal a Najeriya PFN ta bayyana cewa ta bankado shirin da wasu ke yi baiwa Musulmi biyu tikicin takara kujera shugaba da mataimaki a zaben 2023.
Oke ya bayyana cewa duk da kungiyar ba ta zabi wanda zata marawa baya ba, duk jam'iyyar da ke shirin mayar Kiristoci saniyar ware ba zatayi nasara ba.
Yace duk wanda ke kokarin baiwa Musulmi da Musulmi tikiti shaidanin mutum ne kuma dan wuta.
Asali: Legit.ng