Bayan ganawa da Buhari, Gwamna Masari ya bayyana mutanen da suka kashe Kwamishina a Katsina
- Gwamnan Katsina ya jagoranci tawagar dattawan jihar Katsina sun gana da shugaba Buhari a fadarsa dake Abuja
- Bayan wannan ganawa ta sirri, Masari ya bayyana cewa kisan kwamishina Rabe ba shi da alaƙa da ayyukan yan bindiga
- Yace wasu masu kisan gilla ne suka bi shi har gida suka kashe shi, kuma ba da jimawa ba jami'an tsaro zasu gano su
Abuja - Bayan kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Dakta Rabe Nasir, ranar Laraba, gwamnan Katsina, Aminu Masari, yace kisan ba shi da alaƙa da yan bindiga.
Punch ta rahoto gwamnan na cewa ya zama wajibi baki ɗaya jihohin arewa ta yamma su haɗa karfi da ƙarfe wajen magance ƙalubalen tsaro da ya addabi yankin.
Masari ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da manema labarai na gidan gwamnati ranar Talata, bayan ya jagoranci tawagar dattawan Katsina sun sa labule da shugaba Buhari a Aso Villa.
Gwamnan yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Lamarin da ya faru makon da ya shuɗe ba shi da alaƙa da harin yan bindiga, wasu masu kisan gilla da ba'a gano su ba ne suka kashe shi."
"Kuma a halin yanzun jami'an yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki ba dare ba rana domin gano abinda ya faru. Kwamishina na ya rasa ransa a hannun masu kisan gilla kuma ba su ɗauki komai ba a gidansa."
"Saboda haka wannan wani babban laifine dake bukatar a tsananta bincike domin mu gano asalin makasan da kuma dalilin kashe shi."
Wane mataki gwamnati ta ɗauka na gano masakan?
Masari ya tabbatar wa iyalan mamacin da kuma mutanen jihar cewa hukumomin tsaro sun dukufa bincike domin gano masu hannu a kisan gillan.
"Da muka gudanar da bincike kuma muka auna tun bayan matakan da muka ɗauka watanni uku da suka shuɗe, an samu ragin kashi 100 na satar mutane, kashe-kashe da sauran manyan laifuka."
"Saboda haka lamarin da ya faru makon da ya gabata (kashe kwamishina) ba shi da alaƙa da ayyukan yan bindiga."
Wane haɗa kai gwamnoni zasu yi?
Da yake jawabi kan haɗa kai da sauran jihohi, Masari yace a tunaninsa dukkan waɗan nan jihohin fatan su shine su sami nasara a yaƙi da yan bindiga.
Premium times ta rahoto Masari na cewa:
"Ya kamata mu rungumi abinda ke damun mu kuma mu yi aiki tare don tabbatar da mun toshe duk wata kafa.
"Amma idan wannan jihar na da tsarinta, wata kuma nata daban, to ba tantama zasu rinka canza jiha ne daga wannan zuwa wannan."
A wani labarin na daban kuma Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi martani kan kisan kwamishinan kimiyya da fasaha na jiharsa ta Katsina
Shugaban ya yi Allah wadai da lamarin, tare da umartan hukumomin tsaro su baza komarsu wajen kamo masu hannu a kisan.
A ranar Laraba da daddare, wasu da ba'a gano ko su waye ba suka kutsa gidan kwamishinan suka kashe shi.
Asali: Legit.ng