Kawai ka alanta dokar ta baci a jihar Sokoto, Tambuwal ya bukaci Buhari
- Gwamna Tambuwal ya gabatarwa Shugaba Buhari bukatar al'ummarsa don kawar da yan bindiga
- Tambuwal ya bayyana cewa akwai bukatar kafa dokar ta baci ba musamman a jihohin da yan bindiga suka addaba
- Mota mai dauke Akala mutum 42 yan bindiga suka kona kurmus a jihar Sokoto makon da ya gabata
Abuja - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokot ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya alanta dokar ta baci a dukkan wuraren yan bindiga ke ta'adi don kawar da su.
Tambuwal, ya bayyana hakan ne yayinda ya ziyarci shugaban kasan da yammacin Litinin a fadar Aso Villa.
Gwamnan yace wannan bukata zai baiwa Sojoji daman ayyukansu yadda ya kamata kuma bai sabawa kundin tsarin mulki ba.
Mai magana da yawun Tambuwal, Muhammad Bello, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Ya ce a shirya hare-hare na musamman wuraren da yan bindigan ke buya irinsu Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja, da Kebbi.
Hakazalika ya yi kira da Shugaban kasan ya dawo da Sojojin da suka yi ritaya domin su bada gudunmuwarsu wajen wannan yaki.
Buhari ya bada tabbacin za'a dawo da tsaro
Shugaban kasan a jawabinsa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya zata tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Sokoto.
Buhari yace manyan hafsoshin tsarin sun yi masa alkawarin cewa zasu hukunta yan bindigan.
Buhari yace:
"Gwamna Tanbuwal ya yi min bayanin tsaron jihar Sokoto. Na yi masa alkawarin taimakon gwamnatin tarayya wajen dawo da tsaro."
"Ba zamu huta ba har sai wannan ya samu."
Hare-haren Sokoto: Duk laifin Jami'an Sojojin Najeriya ne, Gwamna Tambuwal
A karshen makon da ya gabata, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa shigowar yan bindiga jiharsa daga jihar Zamfara duk laifin jami'an Sojojin Najeriya ne.
Tambuwal ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wakilan Shugaban kasa da suka kai ziyarar jaje jihar Sokoto, rahoton Daily Trust.
A cewarsa:
"Atisayen Operation Hadarin Daji ne ya harzuka rikicin yan bindiga a Sokoto saboda an kora yan bindigan ba tare da taresu daga shiga sauran jihohi ba, irinsu Sokoto."
"Kuma lokacin da akayi harin, jami'an tsaron basu da isasshen kayan aikin da zasu dakile yan bindigan da zasu shiga Sokoto."
Asali: Legit.ng