Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
- Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani sojan bogi wanda ake zarginsa da kwarewa wurin tatsar masu Keke-Napep
- Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wata takardar ya gabatar wa manema labarai a ranar Talata
- A cewarsa, sun samu nasarar damkarsa ne bayan ya gabatar da kansa a matsayin soja, sannan ya kai korafin wani mai Napep akan guduwa da N195,000 dinsa
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Ya bukaci ‘yan sanda su kwatar masa N195,000 daga hannun mai Napep din
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wanda ake zargin ya ce mai Napep din ya tsere da kayan sojojinsa da abubuwansa tsadaddu masu kimar N195,000.”
Kakakin ya ce kwamishinan ‘yan sandan, Sama’ila Shu’aibu-Dikko ya umarci DPO din ofishin ‘yan sandan, CSP Usman Abdullahi akan bincike akan lamarin.
The Nation ta rahoto yadda Kiyawa ya kara da cewa:
“Bincike ya nuna cewa ba sojan gaske bane kuma duk maganganunsa babu gaskiya a cikinsu.
“Bayan ci gaba da bincike an gano cewa zargin da ya yi wa mai Napep din ba gaskiya bane. Ya amsa laifinsa sannan ya bayyana yadda ya dade yana amfani da wannan salon wurin cutar masu Napep."
Asali dan jihar Adamawa ne sojan bogin
Ya kara da cewa asalinsa dan jihar Adamawa ne kuma ya zo har Kano ne don ci gaba da irin wannan damfarar.
Kiyawa ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da sintiri don kama ‘yan ta’adda a cikin jihar.
Kakakin ya shaida yadda aka ci gaba da aiwatar da ‘Operation Puff Adder’ wanda zai taimaka wurin rage miyagun mutane.
Ya bukaci mutane su dinga kai rahoton duk wanda su kama da irin wannan ga lambobi waya kamar haka:
08032419754, 08123821575, 08076091271 ko ya shiga adireshin yanar gizo na “NPF Ruscue me” da ke Play Store.
Kano: Bayan Amsa Gayyatar SSS, Ɗaya Cikin Wadanda Suka Shirya Zanga-Zanga Ta Ce Ta Tsamme Hannunta
A wani labarin, daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar #NoMoreBloodshed a Kano, Zainab Naseer Ahmed, ta ce ta tsame hannun ta daga zanga-zangar, jim kadan bayan fitowa daga ofishin yan sandan farin kaya, SSS.
Tunda farko SSS ta gayyaci Zainab ne domin amsa tambayoyi kan rawar da ta taka wurin shirya zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin arewa da Abuja don janyo hankalin gwamnati kan rashin tsaro a arewa bayan kisar gillar da aka yi wa matafiya 42 a Sokoto.
Bayan shafe kimanin awa biyu a ofishin SSS, Zainab Ahmad ta wallafa a shafinta na Facebook cewa daga yanzu ta tsame hannun ta daga zanga-zangar.
Asali: Legit.ng