Tashin Hankali: An tsinci gawar wani matashi da mace a cikin mota ba tufafi a jikinsu

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani matashi da mace a cikin mota ba tufafi a jikinsu

  • Jami'an tsaron jihar Ogun sun tsinci gawawarki biyu a cikin motar Toyota Camry yayin da suke sintiri da tsakar dare
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu mace da namiji, an gano gawarsu babu tufafi a jikin su
  • Hukumar yan sandan jihar ta bakin kakakinta tace jami'ai na cigaba da bincike amma sun fi zargin wasu ne suka kashe su

Ogun - An tsinci gawar wani mai suna, Azeez Ilias, da wata mace mai suna Deborah a cikin motar Toyota Camry a yankin Ago-Ogun, jihar Ogun.

Tribune ta ruwaito cewa an gano gawar mamatan biyu ne tsirara a cikin mota, kuma tufafin su sun bata, wanda yasa ake kokanton musabbabin mutuwarsu.

Rahotanni sun bayyana cewa daga baya an ga kayan matashin ɗan kimanin shekara 37 a gaban gidansu matar da suke tare.

Kara karanta wannan

Babbar magana: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu bisa wasu laifuka 12

Jihar Ogun
Tashin Hankali: An tsinci gawar wani matashi da mace a cikin mota ba tufafi a jikinsu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jami'an tsaron gwamnatin Ogun, So-Safe Corps, reshen ƙaramar hukumar Idiroko, sune suka gano gawar mutanen biyu ranar Litinin da karfe 2:00 na dare yayin da suka fito sintiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta rahoto Kakakin rundunar So-Safe Corps, Moruf Yusuf, yace:

"Hedkwatar ƙaramar hukumar Idiroko na jami'an tsaron So-Safe Corp mallakin gwamnatin Ogun ta tabbatar wa manema labarai cewa ta gano gawarwaki da misalin ƙarfe 2:00 na daren litinin."
"Namijin mai shekara 37, Azeez Illias, ɗa ne ga shugaban yankin Ipokia, yayin da matar da suke tare aka gano sunanta Deborah."

Ya kara da cewa a halin yanzun jami'an su na kan bincike dan gano musabbabin mutuwar mutanen biyu.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da lamarin, yace da yuwuwar wasu mutane ne suka kashe mutanen biyu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fadarsu da motocinsu

"Eh a halin yanzu muna bincike, muna kokarin gano abin da ya yi sanadin mutuwarsu. Muna zargin wasu ne suka hallaka su, amma zamu bincika."
"Bamu san mai binciken mu zai bayyana ba daga ƙarshe, amma zamu sanar da zaran mun kammala."

A wani labarin kuma Hadimar Buhari ta bayyana Manjo Janar Hamza Al-Mustapha ya tseratad da ita daga yi mata fyaɗe

Shugaban hukumar yan Najeriya dake kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana irin kalubalen da ta shiga ta yadda aka kusa mata fyaɗe lokacin da take aikin jarida.

Tsohuwar yar majalisar tarayya ta shaidawa yan jarida su tashi tsaye kuma su ƙarfafa kansu, su rinka gudanar da binciken kwakkwafi kan wani abu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262