Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din su ta shekarar nan

Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din su ta shekarar nan

WASSCE jarabawar da ta fi kowacce shahara wacce hukumar jarabawar WAEC ta ke gudanarwa, ta na da matukar muhimmanci ga daliban Najeriya.

Sannan ita ce jarabawa ma fi wahala wacce dalibai ke rubutawa kafin su fara makarantun gaba da sakandare.

Sannan su na auna gwargwadon kwazon da dalibai suka samu a matakin A, B, C, D, E da F ga mai kammala makarantar sakandare.

A wannan rahoton, Legit.ng ta tattaro bayanai akan dalibai hudu wadanda sakamakon jarabawarsu ya yi matukar kyau.

1. Victory Yinka-Banjo

A shekarar 2020, dalibar mai shekaru 17 ta shahara bayan ta samu sakamakon A a duk darussan da ta rubuta a WAEC.

Ta wuce wasu jarabawoyin kasashen waje kamar IELTS wanda ta samu sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Gobara ta kama dakin kwanan dalibai a jami'ar Taraba, daliba ta kone kurmus

Jami’o’in Amurka da dama sun bukaci daukar nauyin ta. Sannan bai wuci shekara ba da ta samu damar yin karatu da fiye da dala miliyan 5 daidai da N1,902,500,000 daga jami’o’i daban-daban na Amurka.

Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan
Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan. Hoto daga LinkedIn/Victory Yinka-Banjo
Asali: UGC

2. Ogwubie Chikemzi Praise

Ta samu A a dukkan darussan da ta zauna a 2020.

Yarinyar ta samu nasarar ne a lokacin da hukumar jarabawar ta ce 65.24% ne kadai suka ci jarabawar.

Mutane da dama sun dinga mamakin yadda yarinya mai karancin shekaru ta ke da hazakar gaske. Cikin darussan da ta ci har da Physics, Chemistry da Geography.

Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan
Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan. Hoto daga @IYMTV
Asali: Twitter

3. Praise Ojonugwa Abba

Yaron mai karancin shekarun ya ci jarabawar da kyau inda ya ci A1 a duk darussan da ya rubuta yayin da ya samu B3 daya.

Ya yi karatu a Faith Academy ne a Kaduna kuma ya ci burin karantar fannin likitanci a jami’a.

Legit.ng ta bukaci a tallafa wa yaron don ya samu ya cika burinsa na karantar likitanci a jami’a.

Kara karanta wannan

Yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya tserad da ni daga yi mun fyade, Hadimar Buhari

Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan
Matasan Najeriya 4 da suka nuna bajinta da kwazo a sakamakon WAEC din s ta shekarar nan
Asali: Original

4. Chiemela Stephanie Madu

Sakamakon jarabawar Chiemela ya dauki hankali matuka inda ta samu A a duk darussan da ta rubuta.

Yarinyar ta bayyana burinta na karantar likitanci a jami’ar fasaha ta tarayya a Owerri inda ta samu 345 cikin 400 a jarabawar shiga jami’a.

Ya dace gwamnati ta kawo dauki

Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali akan irin sakamako masu kyau da yara masu kwazo su ke samu don ba su kwarin guiwa ta hanyar tallafa wa karatunsu.

Hakan zai taimaka wurin ba wasu kaimin dagewa wurin yin karatu yadda ya dace da kuma mayar da hankali.

Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta bada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita yanar gizo da labarin rayuwarta mai matukar taba zuciya bayan ta wallafa murnar ta ta tafiya hidimar kasa.

Kara karanta wannan

Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi

A yayin wallafa hotunanta inda ta ke sanye da khakin NYSC, @Teeecookie ta rubuta cewa ta kammala karatun sakandare a shekarar 2009 amma ta dinga bajewa a jarabawar UTME.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: