Ahmad Lawan ya fadi sirri, ya bayyana albashin sanatoci da 'yan majalisun Najeriya

Ahmad Lawan ya fadi sirri, ya bayyana albashin sanatoci da 'yan majalisun Najeriya

  • Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ya fito fili ya bayyana ra’ayinsa game da ma’aunin albashin ‘yan majalisar tarayya
  • Lawan ya kuma nuna matukar jin dadinsa kan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan amincewa da wasu kudirori a tsakanin magabatansa
  • Ya kuma yi cikakken bayani kan yadda ake kashe kudaden gudanar da aiki na ofishin ‘yan majalisar a duk shekara tare da bayyana cewa albashin su ne mafi karancin albashi

Abuja- Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, ya bayyana albashin ‘yan majalisar tarayya da kuma kudaden alawus-alawus da ake biyansu.

Lawan ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ce ya zarce magabatansa wajen amincewa da kudirin doka.

Shugaban sanatocin Najeriya, Ahmad Lawan
Ahmad Lawan ya fadi, ya bayyana albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya | Hoto: Tope Brown
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a cikin wata makala da aka gabatar a jerin lakcocin ‘yan majalisa na farko da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokuradiyya ta kasa ta shirya.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Albashin sanatoci da 'yan majalisar wakilai

Sanatan ya ce albashin Sanata a duk wata Naira miliyan 1.5 ne yayin da na dan majalisar wakilai ya kai Naira miliyan 1.3, kamar yadda BluePrint ta ruwaito.

Ya ce Naira miliyan 13 da aka daura jama a akai shekarun baya a matsayin albashin da Sanata ke karba a duk wata ba komai bane face alawus din su na gudanar da aiki a duk watanni uku.

Lawan ya ce:

"Matsakaicin kudin gudanar da ofis na sanata kusan N13m ne yayin da dan majalisar wakilai ya kai N8m."

Kudin gudanar da ofis na shekara-shekara

Idan aka kididdige kudin ofishin Sanata N13m ya kai N52m duk shekara yayin da na dan majalisar wakilai N8m ya kai N32m a shekara.

Kara karanta wannan

Kasashen musulman duniya sun yi Allah-wadai da babbaka matafiya a Sokoto

An sanya wa laccar Lawan mai taken, 'The Legislature, Legislative Mandate and People – The Reality and the Public Perception.’

Matsayin Lawan akan kudin gudanar da ofis

Ya ce N13m da N8m na gudanar da ofis a duk kwata ga sanata da dan majalisar wakilai, su ne mafi karanci a duk wata kasar dimokuradiyyar a duniya.

Kudaden alawus din kamar yadda ya lissafta, sun shafi kudin tafiye-tafiye na cikin gida/kasa da kasa, tuntubar kwararru, kiwon lafiya, takardun ofis/kwamfutoci, kayan masarufi, littattafai, jaridu, mujallu, kula da motoci da kayan ofis da dai sauransu.

Rochas: Aikin sanata ya fi karfin albashin N13m duk wata, muna bukatar kari

A baya kunji cewa, tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus bai kai yawan wahalar da 'yan majalisar ke yi ba.

Rochas dai ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

Tsohon gwamnan yana kan ra'ayin kada a rage albashin sanataoci, duba da irin kalubalen da suke fuskanta daga mutanen yankunansu na kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.