'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10
- Labarin da muke samu ya bayyana cewa, an samu faruwar wani harin 'yan bindiga a jihar Filato
- Harin na 'yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10, lamarin da ya haifar da firgici a cikin al'umma
- Majiyoyi sun ce, 'yan bindigan sun zo ne daga jihar Zamfara, daya daga cikin jihohin da aka fi samun hare-hare
Jihar Filato - Akalla mutane 10 ne rahotanni suka ce an kashe yayin da wasu da dama suka samu raunuka a yammacin Lahadi a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari garin Pinau da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato.
Lamarin ya faru ne bayan da mutanen kauyen suka kammala kasuwarsu ta mako-mako, The Nation ta ruwaito.
Wani dan unguwar Hamman Sale wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar ana zargin ‘yan jihar Zamfara ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Gabriel Ubah ne ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa rundunar ba ta samu cikakken bayani kan harin ba, kamar yadda AIT ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta
An kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyar su da ke kusa da unguwar Ossra-Irekpeni da ke kan titin Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.
Daya daga cikin mafarautan yankin da suka kai harin ya shaida wa Daily Trust cewa an yi musayar wuta dasu.
Ya ce mafarautan tare da shugaban karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi, Joseph Samuel Omuya, sun kai farmaki dajin ne bisa samun rahoton kasancewar 'yan ta'addan a yammacin Laraba.
Majiyar ta ce a lokacin da suke kutsawa dajin, masu garkuwar sun bude wuta inda mafarautan suka mayar musu da wuta.
A wani labarin, ‘yan bindiga a jihar Zamfara sun fito da sabon salo mai hatsarin gaske yayin da suka bukaci a biya sama da Naira miliyan 1 a matsayin haraji kan yankuna daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin-Magaji na jihar.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Mazauna wadannan yankuna an ce yanzu haka suna cikin karkashin ‘yan bindigar da suka kafa gwamnatinsu a yankunan da lamarin ya shafa.
Asali: Legit.ng