Da duminsa: Sojoji sun fitittiki yan bindigan da suka kai hari Kaduna cikin dare

Da duminsa: Sojoji sun fitittiki yan bindigan da suka kai hari Kaduna cikin dare

  • Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sake kai hari jihar Kaduna don awon gaba da mutane
  • Mutan unguwar sun tsallake rijiya da baya yayinda Sojoji suka kawo musu dauki
  • Bayan sa'a guda ana musayar wuta da Soji, yan bindigan sun gudu da kafafunsu

Kaduna - Yan bindiga sun kai hari unguwar Sabon Tasha, karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna cikin daren Asabar, 11 ga watan Disamba, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan bindigan sun banka wuta gidan wani mutumi bayan kokarin garkuwa da shi.

Jami'an Sojojin Najeriya sun samu nasarar fitittikarsu bayan kirar da wani yayi musu.

An tattaro cewa Sojoji da yan bindigan sun yi musayar wuta misalin karfe daya na dare.

Jihar Kaduna cikin dare
Da duminsa: Sojoji sun fitittiki yan bindigan da suka kai hari Kaduna cikin dare
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Tsagerun yan bindiga sun sake tasa keyar dandazon mutane a jihar Kaduna

Wani mai idon shaida, Benjamin, ya bayyanawa Daily Trust cewa yan bindiga na kokarin shiga gida-gida kwashe mutane lokacin da Sojoji suka isa.

Yace:

"Mun godewa Allah Sojojin sun isa da wuri, da abin yayi muni saboda sun shiga sace mai gidan ne amma babu kowa a gidan, sai suka banka wuta cikin fushi."

Manema labarai sun tattaro cewa sai da aka kwashe awa guda ana musayar wuta tsakanin yan bindigan da Sojoji.

Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

A makon da ya gabata, Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda akayi awon gaba da mutane 50 yayinda yan bindiga suka kai hari Unguwar Gimbiya dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Wani mai idon shaida wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa manema labarai cewa wannan hari ya auku ne da sanyin safiyar Juma'a, 3 ga Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

A cewarsa yan bindigan sun kai gari gidaje akalla 13 kuma sai da suka kwashe sa'o'i biyu suna diban jama'a.

"Sun kai garmaki Ungwan Gimbiya dake Sabo, karamar hukumar Chikun dake Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace 50," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: