Da duminsa: An damke Diraktan ma'aikata a jihar Kano yana tsakiyar karbar cin hanci
- Mako daya bayan damke shugaban hukumar CPC a Kano, an damke babban dirakta a ma'aikatar
- Mutumin da aka baiwa hakkin tabbatar da ingancin kayayyaki don amfanin jama'a ya shiga hannun yana karban rashawa
- Hukumar ya ki da rashawan Kano ta bayyana cewa Diraktan na tsare hannun su yanzu haka
Hukumar amsa korarrafi da yaki da rashawa a jhar Kano (PCACC) ta damke Diraktan tabbatar da ingancin kayayyaki na hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki CPC, Mr Bello Alkarya, wanda aka fi sani da 'Najeriya'.
Daily Trust ta ruwaito cewa an damke Alkarya ne yana tsakiyar karbar cin hani hannun wasu mukaddashin Shugaban hukumar, Barista Mahmud Balarabe, ya bayyana hakan
A cewarsa:
"Yana tsare hannunmu bayan mun kama shi dumu-dumu yana karbar kudi, muna bincike kan lamarin amma yana tsare hannunmu."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jami'an DSS sun damke shugaban hukumar CPC, Janar Dambazau a Kano
Kimanin mako guda kenan da, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi ram da shugaban hukumar Consumer Protection Council (CPC) na jihar Kano, Janar Idris Dambazau, bisa zargin yiwa tattalin arziki zagon ƙasa.
A rahoton Vanguard, wata majiya dake kusa da jami'an tsaro tace, DSS na zargin Janar Dambazau da garƙame gidajen man fetur 7, ba tare da bin ƙa'ida ba.
Haka nan kuma majiyar ta ƙara da cewa an yi kokarin sa Janar Danbazau ya buɗe waɗan nan gidajen man fetur amma ya yi kunnen uwar shegu da zancen.
Asali: Legit.ng