Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu

  • Daya daga cikin matafiyan da ta rayu bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan nan masu zuwa kudu daga Sokoto ta magantu
  • A cewarta, a gaban idanunta ‘yan bindigan su ka kona mahaifiyarta, yaranta hudu da kuma wasu ‘yan uwanta har su ka zama toka
  • Yanzu haka matar, mai suna Shafa’atu ta na asibiti ana kulawa da lafiyarta sakamakon miyagun raunukan da ta samu ta dalilin kunar

Sokoto - Wata mata mai shekaru 30, wacce ta tsira bayan harin da ‘yan bindiga su ka kai wa matafiyan hanyar Kaduna da su ka doshi kudu ta bayyana yadda mahaifiyarta da yaranta 4 su ka kone kurmus, Daily Trust ta ruwaito.

Matar mai suna Shafa’atu, cikin matafiyan ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.

Kara karanta wannan

Tirelar Da Jami’an Kwastam Su Ka Biyo Ta Afka Wa Wata Mata Da Yaranta 3

Harin Sokoto: Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu, Shafa'atu
Ina kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiya ta da 'ya'ya na 4 da ransu a Sokoto, Shafa'atu. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shafa’atu, wacce yanzu haka take asibiti inda ake kulawa da lafiyarta sakamakon kunar da ta yi, ta yi hira da manema labarai duk da halin da ta ke ciki.

Ta ce akwai manya 33 da yara da dama a cikin motar

A cewarta, a cikin motar akwai manya 33 da yara da yawa lokacin da ‘yan bindigan da ake zargin yaran Bello Turji, ‘yan bindigan da su ka addabi arewacin Sokoto, ne su ka kai musu farmakin.

Kamar yadda ta shaida:

“Sun dinga harbin motar mu har sai da ta mulmula sau uku sannan ta kama da wuta. Cikin hukuncin Ubangiji daga ni sai wani fasinja ne mu ka tsira amma duk sauran sun mutu saboda harbin da ya same su.

Kara karanta wannan

Mafarauta Da Ƴan Sa Kai Sun Ceci Matafiya Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane, Sun Kama 2

“Na rasa yara na hudu, uku duk sun girma da kuma jariri mai watanni goma. Ina kallonsu har da mahaifiyata, kawuna da yaran yayyina duk su ka kone kurmus yayin da ‘yan bindigan su ke kallonmu cike da nishadi.”

Ta kasa ci gaba da bayani saboda mummunan yanayin da ta ke

Sai dai ana wannan gabar ne Shafa’atu ta dakata da magana sakamakon mummunan yanayin da ta ke ciki.

Daily Trust ta gano yadda Shafa’atu da ‘yan uwanta suka kwashe ya nasu ya nasu saboda addabarsu da ‘yan bindigan su ka yi a yankin.

Kawunta wanda ya ke kula da lafiyarta a asibiti ya ce shi ya jagoranci birniyar yaran.

A cewarsa:

“An dawo da ragowar gawawwakin su a cikin motocin asibiti, amma ba mu iya bambance gawawwakin. Mun yi duk wasu addu’o’in da su ka dace sannan mun birne su kamar yadda adininmu ya tanadar.”

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

A wani labarin, Kwamishinan 'yan sandan Jihar Sokoto, CP Kamaludeen Okunola, ya tabbatar da cewa an kashe mutum 23 yayin harin da aka kai wa matafiya a Angwan Bawa a karamar hukumar Sabon Birni na Jihar.

Okunola, wanda ya tabbatar da adadin a jiya, bayan taron tsaro da Gwamna Aminu Tambuwal, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, ya kara da cewa an tura jami'ai su binciko wadanda suka aikata.

Kakakin yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar, ya bada labarin yadda yan bindigan suka kai wa motar da ke dauke da fasinjoji 42 hari, hakan ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 18.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164