'Ba zata saɓu ba,' Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan Kwamishina a jihar Katsina
- Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi martani kan kisan kwamishinan kimiyya da fasaha na jiharsa ta Katsina
- Shugaban ya yi Allah wadai da lamarin, tare da umartan hukumomin tsaro su baza komarsu wajen kamo masu hannu a kisan
- A ranar Laraba da daddare, wasu da ba'a gano ko su waye ba suka kutsa gidan kwamishinan suka kashe shi
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da kisan kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina, Dakta Rabe Nasir.
Buhari ya bayyana lamarin da babban abin takaici kuma abin Allah wadai, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
A wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya jaddada cewa ba zata saɓu ba, kuma gwamnatinsa ba zata bar kafar da irin haka zata rinka faruwa a kasar nan ba.
Shugaban yace yaji bakin ciki da takaici ya kama shi game da lamarin na kashe shugaba nagari mai tasowa, wanda ke wa al'ummarsa, jiha da ƙasa aiki cikin himma da kwazo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Buhari yace:
"Ina miƙa jaje na ga iyalan marigayin. Sannan kuma muna rokon hukumomin tsaro su tsananta bincike domin tabbatar da an hukunta masu hannu a wannan ta'addancin."
Yadda lamarin ya faru
A ranar Laraba da daddare, wasu da ba'a san ko suwaye ba suka hallaka kwamishina Dakta Nasir, a gidansa dake jerin gidaje na Fatima Shema Estate kan hanyar Daura a birnin Katsina.
A cewar wasu majiyoyi, an kashe kwamishinan ne a cikin wasu awanni na dare, kuma maharan sun kulle gawarsa a ban daki.
Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa jami'ai sun kama mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu a kisan, kuma sun tabbatar da cewa suna kan aikin bincike a halin yanzu.
A wani labarin na daban kuma Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci gidan da aka kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Rabe Nasir.
Rahoto ya bayyana cewa bayan maharan sun kashe shi, sun ja gawarsa zuwa ban ɗaki kuma suka garkame kofar.
Asali: Legit.ng