'Yan Banga a Kaduna sun fita zanga-zanga kan kama kwamandansu
- 'Yan bangan jihar Kaduna sun fito zanga-zanga kan kama kwamandansu, Aminu Sani, wanda jami'an rundunar sojin Najeriya suka yi
- Kamar yadda kwamandan shiya ta 1, Usman Abdullahi ya sanar, ya ce ba su san dalilin kama shugabansu ba kuma har yanzu ba a san inda aka adana shi ba
- A wata majiya ta daban, an gano cewa an kama kwamandan 'yan bangan ne sakamakon zarginsa da ake yi da hannu wurin taimakon 'yan bindiga
Kaduna - 'Yan bangan jihar Kaduna a ranar Alhamis sun fito zanga-zanga akan kamen kwamandansu , Aminu Sani wanda aka fi sani da Bolo.
Jami'an rundunar sojin Najeriya ne suka kama Bolo a gidansa kwanaki 15 da suka gabata kuma har yanzu ba a san inda suka yi da shi ba, Daily Trust ta ruwaito.
Daily Trust ta tattaro cewa, sojojin sun kama kwamandan 'yan bangan ne a yankin Rigasa tare da wasu matasa biyu amma an sako matasan bayan sa'a daya da kamen.
Kwamandan 'yan bangan na shiya ta daya, Usman Abdullahi, yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan zanga-zangar a ofishinsa da ke Rigasa ta karamar hukumar Igabi, ya ce duk wani kokarin ganin sun san inda aka kai kwamandan ya tashi a tutar babu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce babu wanda ya sanar da su dalilin kama shi wanda hakan ne yasa suka fito zanga-zanga domin dalilin kamen.
"Mun tabbatar ya na hannun sojoji saboda su ne suka kama shi a kwanaki 15 da suka gabata, mun yi kokarin sanin abinda yayi amma an hana mu ganin shi," yace.
Kamar yadda yace, sun fito zanga-zangar ne domin su bayyana damuwarsu kan kama shi da aka yi.
Wata mambar kungiyar mai suna Linda John, ta kwatanta kwamandan jihar da zama mutum nagari wanda ya mayar da hankali wurin yaki da ta'addanci.
Ta yi kira ga gwamnati da ta shiga lamarin wurin gano inda shugabansu yake kuma ta tabbatar da cewa ya dawo gida cikin iyalinsa.
A yayin da aka tuntubi mataimakin daraktan yada labarai na Div 1, Kanal Ezindu Idmah, ya yi alkawarin kira bayan ya gano bayanan komai amma har a yayin rubuta wannan rahoton bai kira ba.
Asiri ya tonu: Sojoji sun cafke Shugaban ‘Yan banga bisa zargin alaka da ‘Yan bindiga
A wani labari na daban, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Rundunar sojojin kasan Najeriya ta bada sanarwa game da shugaban ‘yan bangan da ta kama a yankin Rigasa.
A wata sanarwa da ta fito daga bakin mukaddashin darektan yada labarai na sojoji, Birgediya Janar Benard Onyeuko, an tabbatar da kama Mal. Aminu Sani.
A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, Janar Benard Onyeuko ya shaidawa manema labarai cewa sojoji sun yi ram da Aminu Sani wanda aka fi sani Bolo.
Asali: Legit.ng