Yanzu-Yanzu: Gwamnati ta buɗe hanyoyin sadarwa da aka datse a jihar Katsina
- Bayan kwashe wata uku da rufe layukan sadarwa a jihar Katsina, gwamnati ta bada umarnin dawo da shi yau Alhamis
- A sanarwan da hadimin gwamna Masari kan harkokin tsaro ya fitar, yace an ɗauki wannan matakin ne saboda samun saukin ayyukan yan bindiga
- Yace dama an ɗauke sabis na wani ɗan lokaci ne a kokarin gwamnatin Masari na dakile yan bindiga da masu taimaka musu
Katsina - Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta sanar da dawo da amfani da layukan sadarwa a sassan jihar.
Rahoton Aminiya Hausa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dawo da sabis da ta datse a baya a yunkurin dakile yawaitar ayyukan yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Gwamnati ta ɗauki matakin datse hanyoyin sadarwa da wasu matakai ne a wasu kananan hukumomin jihar domin yaki da ta'addancin yan bindigan daji.
Babban mai baiwa gwamna Masari shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Ibrahim Muhammad Katsina, shine ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar.
Meyasa za'a dawo da sabis Katsina?
Bayan shafe watanni uku da rufe hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 17, da rufe wasu kasuwanni, wanda gwamnatin jihar Katsina ta yi, ta bada umarnin sake bude su.
A cewar hadimin gwamna, gwamnatin Katsina ta ɗauki wannan matakin ne bayan gano cewa an samu saukin ayyukan ta'addancin yan bindiga da kuma masu kwarmata musu bayanai.
Yace:
"Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa ne na wani lokaci, da nufin dakile ayyukan yan bindiga da masu taimaka musu da bayanai, musamman a waɗan nan kananan hukumomi 17."
Daga ƙarshe, Mashawarcin gwamnan ya yi kira ga Katsinawa su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya a kokarinta na ganin ta magance matsalar tsaron da ta addabi jihar.
A wani labarin na daban kuma bayan hatsarin kwalekwale da ya faru a Kano, Gwamnatin Ganduje ta dakatar da sufurin jiragen ruwa a Bagwai
Gwamnatin Kano ta sanar da ɗaukar matakin dakatar da sufurin jiragen ruwa a yankin karamar hukumar Bagwai.
Rahoto ya nuna cewa a zaman majalisar zartarwa, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciko musabbabin hatsarin da ya lakume sama da rai 20.
Asali: Legit.ng